Abokin Takarar Obi, Datti Baba-Ahmed Ya Fadi a Rumfar Zabensa, Atiku Ya Kawo Akwatin
- Datti Baba-Ahmed, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP, ya sha kaye a akwatin zabensa
- Jam'iyyar PDP ta su Atiku Abubakar ta lashe zabe a rumfar zaben ta PU 021 da ke gudunmar Tudun Wada, karamar hukumar Zaria, Kaduna
- Ana nan ana ci gaba da tattara sakamakon zaben na shugaban kasa wanda ya gudana a fadin Najeriya a yau Asabar
Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed, ya sha kaye a rumfar zaben da ya kada kuri'arsa a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna..
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne ya yi nasara a rumfar ta Baba-Ahmed, jaridar The Cable ta rahoto.
Abokin takarar na Peter Obi ya kada kuri'arsa ne a rumfar zabe ta PU 021 da ke gudunmar Tudun Wada, karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna.
An dai tantance masu zabe 272 a zaben shugaban kasar da ke gudana a fadin kasara yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Adadin kuri'un da kowani dan takara ya samu
Atiku ya samu kuri'u 102 wajen kawo akwatin zabe inda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya biyo bayansa da kuri'u 98.
Jam'iyyar Labour Party ita ta zo ta uku da kuri'u 54 yayin da dan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zo na hudu da kuri'u 11,.
Jam'iyyar Accord ta yi maja da Labour Party a ranar zaben shugaban kasa
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa jam'iyyar Accord ta rushe tsarinta a ranar zabe inda ta yi hadaka da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Mista Peter Obi.
Shugabancin jam'iyyar ta Accord ya ce sun koma bayan Obi ne domin suna da yakinin cewa zai lashe zaben shugaban kasar na yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Ana dai fafatawa a zaben shugaban kasar tsakanin manyan yan takara da suka hada da Atiku Abubakar, Peter Obi, Bola Tinubu da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Legit.ng