Zaben Shugaban Kasa: Yan Daba Sun Tarwatsa Masu Zabe a Wata Rumfar Zabe a Jihar Lagas
- Jama'a sun shiga tashin hankali a yankin Ikate da ke jihar Lagas bayan wasu bata gari sun far masu a wajen zabe
- Yan daban sun lalata tare da sace kayan zabe bayan sun fatattaki jama'a da jami'an hukumar zaben
- A yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da na yanmajalisun tarayya a fadin Najeriya
Lagos - Masu zabe a yankin Ikate da ke jihar Lagas basu samu damar aiwatar da yancinsu na yan kasa ba ta hanyar yin zabe a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Hakan ya kasance ne bayan wasu bata gari da ake zaton yan dabar siyasa ne sun farmaki rumfar zabensu sannan suka fatattaki jama'ar da suka taru domin yin zabe tare da lalata kayan zaben.
A cewar wasu da abun ya faru a kan idanunsu, lamarin ya shafi rumfar zabe ne da ke kusa da fadar sarkin Elegushi, jaridar Vanguard ta rahoto.
Sai mun yi zabe za mu tafi, masu kada kuri'a
Sai dai kuma, masu kada kuri'ar da ke kokarin takewa yanci sun dage lallai sai sun aiwatar da yancinsu kafin su bar rumfar zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
PM News ta kuma rahoto cewa rumfunan zabe hudu yan daban suka farmaka kuma hakan ya haifar da tashin hankali a yankin inda mutane suka dunga gudun tsira.
An kuma tattaro cewa maharan sun tsere da akwatunan zabe sannan suka fatattaki jami'an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.
Yan daba sun farmaki rumfar zabe a Kogi, sun bindige wani matashi
A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa wasu bata gari sun kai hari rumfar zabe a Anyigba da ke kamaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi yayin da mutane suka taru don kada kuri'unsu.
Maharan suna ta harbi kan mai uwa da wahabi inda aka yi rashin sa'a harbin bindiga ya samu wani matashi da ya je yin zabe tare da aika shi lahira.
Wannan tashin hankali da aka samu a yankin Kogi ta gabas ya yi sanadiyar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta soke zabe a rumfunar zabe guda bakwai.
Asali: Legit.ng