Obi Ya Kara Samun Karfi: Jam'iyyar Accord Ta Janyewa Labour Party Yan Awanni Kafin Zabe

Obi Ya Kara Samun Karfi: Jam'iyyar Accord Ta Janyewa Labour Party Yan Awanni Kafin Zabe

  • Yayin da masu zabe suka tsunduma a zaben shugaban kasa na 2023, abubuwa na kara sauya salo a siyasar kasar
  • Sabbin rahotanni sun bayyana cewa shugabancin jam'iyyar Accord ya saki wata sanarwa inda yake ayyana goyon bayansu ga Peter Obi
  • Shugaban jam'iyyar, Rev Isaac Adeniyi, ya ce sun gamsu cewa dan takarar na Labour Party zai yi nasara a zaben

Jam'iyyar Accord ta sanar da cewar za ta janye takararta na shugaban kasa don goyon bayan takarar shugabancin Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, jam'iyyar ta yanke hukunci ne a jajiberin ranar zabe kafin fara zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Peter Obi rike da lasifika yana jawabi
Obi Ya Kara Samun Karfi: Jam'iyyar Accord Ta Janyewa Labour Party Yan Awanni Kafin Zabe Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

An tattaro cewa shugabancin jam'iyyar ya fitar da wata wasika kan haka kuma ya gabatar da shi ga manema labarai a daren ranar Juma'a, 24 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Abuja Ya Mutu a Ranar Zabe

Jam'iyyar Accord ta yi maja da Labour Party

A cewar rahotanni, wasikar ya nuna shirin jam'iyyar na yin hadaka da Peter Obi da Labour Party.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta tattaro cewa jam'iyyar Accord ta sha alwashin cewa za ta gabatar da manyan cibiyoyinta ga Peter Obi a fadin kananan hukumomi 774 na kasar.

Da aka tuntube shi, Rev Isaac Adeniyi, shugaban jam'iyyar ta Accord, ya tabbatar da ci gaban yana mai cewa:

"Mun yarda Obi na da damar lashe zaben nan na shugaban kasa."

Shugaban kasa a 2023: Primate Ayodele ya bayyana wanda zai ci zabe

A wani labari na daban, babban faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ne zai lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da Dan Majalisar PDP Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Farmakin Neman Ransa

Da yake bayyana hakan yan kwanaki kafin zabe, Primate Ayodele ya yi ikirarin cewa ba wai ra'ayinsa yake fadi ba, illa abun Allah ya nuna masa game da babban zaben kasar.

Ya ce Allah ya zabi Atiku don aiwatar da babban aiki na fitar da kasar daga mawuyacin halin da take ciki, cewa idan bar ba'a zabe shi toh yan Najeriya za su sha wahalan da ya fi wanda suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng