An Gano Daruruwan Katunan Zabe a Hotel a Legas Ranar Zabe
- Duk da wahalar da jama'a ke sha wajen samun katin zaɓe, an gano daruruwan PVC a wani Otal a jihar Legas
- An samu wannan ci gaban ne a ranar zabe yayin da yan Najeriya ke shirin yanke wanda zai gaji shugaba Buhari yau Asabar
- Nan take bayan ganin daruruwan katunan, mutanen karamar hukumar Oshodi Isolo sun mamaye Otal ɗin don duba katunansu
Lagos - An tsinci daruruwan katunan zaɓe watau PVC a wani Otal da ke Ago Palace Way, yankin Ilasamanja, ƙaramar hukumar Ishodi Isolo a jihar Legas.
Hakan na kunshe ne a wani Bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Shafin dandalin sada zumunta, @UbongabCardinal ne ya wallafa bidiyon ranar jajibirin zaben shugaban kasa da daddare, watau Jumu'a 24 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan
Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 a Wata Jihar Arewa Suna Shirin Kawo Tsaiko Ga Sakamakon Zabe
Sakon ya nuna cewa:
"Idan mazabarka na karkashin ƙaramar hukumar Ishodi/Isolo kuma har yanzun baka karbi katin zabenka ba, ka garzaya Nobis Otal da ke Ago Palace Way, Ilasamanja, jihar Legas, ka duba katinka."
"Obidiet (magoya bayan ɗan takarar Labour Party, Peter Obi) ba zasu karaya ba kuma ba mai ɗauke masu hankali, mu zamu ci zaɓen nan."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Muhimmin abin lura: Ya na da kyau ku sani har zuwa lokacin kawo maku wannan rahoton, Legit.ng Hausa ba ta tabbatar da sahihancin bidiyon ba.
A yau ne yan Najeriya daga kowane bangare zasu zabi wanda suka amince ya ci gaba da mulkarsu bayan kammala wa'adin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Ana hasashen ɗaya ɗaga cikin yan takara huɗu ne zasu iya ba da mamaki, Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar, na PDP, Rabiu Kwankwaso, ma NNPP da Peter Obi na Labour Party.

Kara karanta wannan
2023: Manyan Kalubale Uku da Muke Fuskanta a Zaben Ranar Asabar, Sufetan Yan Sanda
Akwai matsala babba gaban Atiku
A wani labarin na daban kuma an gano Babban Abinda Zai Ja Wa Atiku Faɗuwa Zaben Shugaban Kasa 2023
Wani fitaccen lauya ya yi hasashen cewa tarin rashin nasara ka iya maimaita kansa kan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
A cewarsa rikicin cikin gida da ya addabi babbar jam'iyyar jamayya da kuma yadda ya zabi abokin takararsa na cikin abubuwan da zasu kai Atiku ƙasa.
Asali: Legit.ng