Har Yanzun Kungiyoyin Yan Ta'adda Uku Barazana Ne Ga Zaben Asabar, IGP

Har Yanzun Kungiyoyin Yan Ta'adda Uku Barazana Ne Ga Zaben Asabar, IGP

  • Sufetan 'yan sanda na ƙasa, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana kalubalen da zaben Asabar ke fuskanta
  • Usman Baba ya ce rundunar yan sanda ta shirya tsaf don tabbatar da zaben ya gudana cikin zaman lafiya
  • A yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu, yan Najeriya zasu zabi shugaban kasa, Sanatoci da mambobin majalisar wakilai

Abuja - Awanni gabanin fara zaben shugaban kasa da ake dako, Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan kasar nan, Usman Alkali Baba, ya ce har yanzun akwai kalubale.

Usman Baba ya ce ayyukan yan fashin daji, 'yan ta'adda da haramtacciyar ƙungiyar yan aware watau IPOB ko mayakanta ESN barazana ce ga zaben Asabar.

IGP Usman Alkali Baba.
Har Yanzun Kungiyoyin Yan Ta'adda Uku Barazana Ne Ga Zaben Asabar, IGP Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

IGP ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi, Tinubu: Daga Karshe Malamin Addini Ya Bayyana Magajin Buhari a Zaben Gobe Asabar

"Har yanzun muna kallon ayyukan yan fashin daji, yan ta'adda da kuma masu fafutukar tsinke wa watau IPOB ko ESN a matsayin kalubale," inji Usman Baba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa dabancin siyasa da faɗace-faɗace tsakanin jam'iyyu duk suna cikin abinda su ke zama kalubale ga zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Bugu da ƙari, Sufetan ya bayyana hare-haren da ake kaiwa ofisoshin INEC su ma kalubale ne.

Ya ce rundunar 'yan sanda ba ta amince sauran jami'an tsaron da jihohin suka kafa ko wasu mutane kamar Amotekun Corps a kudu maso gabas, su yi aiki a wurin zaɓe ba.

"Na ba da umarnin kar a bar hukumomin tsaron masu zaman kansu su yi aiki a wuraren zaɓe," inji IGP.

Ya kuma jaddada cewa rundunar yan sanda ta shirya tsaf domin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe. Ya ce jami'ai 425,106 aka tura aikin zaben shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya.

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Bayan lissafa kalubalen da ake zaton zasu iya kawo cikas a zaɓe, Sufeta Janar ya bayyana cewa hukumar yan sanda ta gama shirin ba da ingantaccen tsaro yayin zaɓe.

An kama wani mutum dauke da takardun naira

A wani labarin kuma An Kama Wani Mutum Da Maƙuden Miliyoyin Naira A Mota Zai Kai Wa Ɗan Siyasa A Gombe

Wannan kame na zuwa ne yayin da ya rage awanni 'yan Najeriya su zabi shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262