Tinubu/Shettima Za Su Shiga Zabe da Goyon Bayan Tsofaffin Jam’iyyun Siyasa 65
- Jam’iyyun nan da aka karbe masu lasisin rajista sun ce ‘dan takara daya ne ya cancanta a 2023
- Kolawole Ajayi ya ce wannan mutum guda shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC
- A cewar Ajayi, ‘dan takaran APC zai iya kawo cigaba kuma gwamnatinsa za ta hada-kan jama’a
Lagos – Tsofaffin jam’iyyun siyasa 65 suka yi mubaya’a ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai neman mulkin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC.
The Nation ta rahoto cewa wadannan jam’iyyu da aka sokewa rajista sun tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a zaben shugabancin kasa.
Shugaban kungiyar jam’iyyun, Kolawole Ajayi, ya shaida cewa jam’iyyu 65 da aka soke rajistarsu a Najeriya, za su marawa ‘dan takaran na APC baya.
Cif Kolawole Ajayi yake cewa sun dauki wannan matsaya ne bayan la’akari da cewa a duk cikin masu neman shugabanci a 2023, Tinubu ya fi dacewa.
Tsohon shugaban majalisar IPAC ta jam’iyyun ‘yan siyasa na reshen jihar Legas ya ce sun duba tarihin da 'dan siyasar ya bari a inda ya yi aiki a rayuwa.
Mutum 1 ya yi fice a 'yan takaran 2023
An rahoto Ajayi yana mai cewa a cikin wadanda suke harin lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fubrairu, mutum daya ne ya cancanta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
‘Dan siyasar ya ce ba kowa ba ne wannan illa tsohon Gwamnan na jihar Legas mai takara a APC.
A sakamakon wannan mubaya’a, daukacin shugabanni da mabiya wadannan jam’iyyu da aka karbewa lasisi, za su tabbatar da nasarar APC a ranar Asabar.
Jawabin Cif Kolawole Ajayi
"Bayan jeringiyar tattaunawar masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisar amintattu, mun gamsu mutum daya ne a cikin ‘yan takaran nan yake da abin da ake bukata wajen zurfafa damukaradiyya, kawo cigaba da hadin kan kasa da jama’arta.
Wannan mutum guda shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A dalilin haka, a yau mu ke yi masa mubaya’ar takarar shugaban kasa, kuma mu tabbatar da duka shugabanninmu da magoya bayan jam’iyyu 65 da aka sokewa rajista da suke wajen taron nan, za su tabbata Asiwaju Tinubu ya samu nasara a zaben shugabancin kasa.
An hana Abba Kyari beli
A yayin da ake shirin zaben sabon shugaban kasa, kun samu labari cewa jami’in 'Dan sandan, DCP Abba Kyari zai cigaba da zama gidan gyaran hali.
Alkalan kotun daukaka kara sun gamsu da hukuncin babban Kotun tarayya da ta ce a rike Abba Kyari. Stephen Adah da biyu sun ki yarda a ba shi beli.
Asali: Legit.ng