Haramun Ne Zuwa Da Wayar Salula Inda Ake Kaɗa Ƙuri'a, INEC

Haramun Ne Zuwa Da Wayar Salula Inda Ake Kaɗa Ƙuri'a, INEC

  • Ana dab da a fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen Najeriya, hukumar INEC ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa
  • Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta bayyana cewa ta haramta masu zaɓe yin wani abu a lokacin zaɓen
  • Hukumar INEC ta kuma ƙara haske kan shirye-shiryen da take yi domin gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya

Abuja- A yayin da ake shirin fara gudanar da babban zaɓe a Najeriya, hukumar zaɓw mai zaman kanta (INEC) ta bayyana wata muhimmiyar doka ga masu kaɗa ƙuri'a.

Hukumar zaɓen ta bayyana cewa ta haramtawa masu yin zaɓe zuwa wajen da aka ware domin kaɗa ƙuri'a da wayar salula. Rahoton Channels Tv

Yakubu
Haramun Ne Zuwa Da Wayar Salula Inda Ake Kaɗa Ƙuri'a, INEC Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shine ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

Shugaban hukumar zaɓe ya kuma nuna damuwar sa kan siyan ƙuri'a a lokacin zaɓen na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Saki Adadin Wadanda Suke Karbi Katin Zabe, Masu Kaɗa Ƙuri'a a Zaɓen 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai shugaban ya bayyana cewa yana fatan za a magance matsalar ta siyan ƙuri'a.

Shugaban ya kuma bayyana cewa an raba kayayyakin aikin zaɓe ga dukkanin jihohin ƙasar nan, inda yanzu haka ake raba muhimmin kayan aikin zaɓen ga ƙananan hukumomin ƙasar nan.

Shugaban na INEC ya kuma ƙara nanata cewa wuraren zaɓe 240 ne ba su da masu yin zaɓe.

Haka kuma Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa katin zaɓe na din-din-din (PVC) miliyan tamanin da bakwai (87m) ne aka karɓa kafin zaɓen. Rahoton Daily Trust

The INEC ya kuma ƙara bayyana cewa wakilan zaɓe 1,642,385 na jam'iyyun siyasa ne za su shiga cikin zaɓen.

Jihohin Da Manyan Ƴan Takara 4 Zasu Lashe Babu Tantama a Zaɓen 2023

A wani labarin na daban kuma, hasashe ya nuna jerin jihohin da manyan ƴan takarar shugaban ƙasa zasu lashe babu tantama a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Saura Kwana Biyu Zaɓe, Tinubu Yayi Wani Babban Kamu A Abuja

A zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar akwai manyan ƴan takara 4 dake kan gaba waɗanda ake yuwa kallon ɗaya daga cikin su shine zai zama zakara a zaɓen na ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng