Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Jam’iyyun Adawa da ‘Yan Takararsu a Mintin Karshe
- A yau aka ji Jam’iyyun ZLP, NRM, APP, APM a Legas sun ce Bola Tinubu ne ‘dan takaransu a 2023
- Shugabannin jam’iyyun za su marawa Bola Tinubu/Kashim Shettima baya su karbi mulkin Najeriya
- ‘Yan adawan sun lissafo hujjojin da suka jawo su ke ganin cancantar Jagaban kan sauran ‘yan takara
Lagos - Jam’iyyun siyasa akalla goma da kuma ‘yan takararsu suka yi wa Bola Tinubu mubaya’a, su na goyon bayan ya zama shugaban kasa.
Rahoton Tribune ya ce jam’iyyun nan sun hada da ZLP, NRM, APP, APM da sauransu, sun bayyana haka a wani taro da aka yi a Ikeja a jihar Legas.
Shugabar jam’iyyar hamayya ta NRM ta reshen Legas, Temilola Akinade ta ce sun tsaida ‘dan takaran ne domin sun fahimci shi ya fi cancanta.
Akinade tayi jawabi a asibitin filin tashin jirgin Ikeja a madadin sauran shugabannin jam’iyyu ta ce sun yi mubaya’a ne ga tikitin Tinubu/Shettima.
Meyasa sai Tinubu?
Jaridar ta ce dalilin shugabar NRM na daukar matsayar nan ita ce Bola Tinubu yana goyon bayan tsarin tarayya kuma ya yarda jihohi su kafa ‘yan sanda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jan’iyyun sun ce tsohon Gwamnan na Legas mutum ne da ya yi imani da adalci da hadin-kan kasa, kuma zai kawo cigaba domin ya fahimci tattalin arziki.
A rahoton Sun, Adekunle Adenipekun wanda shi ne shugaban jam’iyyar ZLP ya ce Tinubu zai magance matsalolin tsaron da ake fama da su a kasar nan.
Benedict, Onyebuchi Chioma, Mayowa Ola, Adenipebi Abosede, Ifako Ijaiye, da Sotonwa Adebayo, suka wakilci ‘ya 'yan jam’iyyar ZLP na jihar Legas.
Sauran sun hada da; Lukman Adebola, Alimosho, Hassan Ramon, Ajeromi Ifelodun, AbdulGaniu Taiwo, Orji Blessing, Hon.Uba Oluchi da Anthony Emeriole.
Tinubu garau yake?
Mahalarta taron sun ce sun tabbatar da cewa tsohon Gwamnan na jihar Legas yana da koshin lafiya, kuma ba wani aikin karfi zai je yi a fadar Aso Rock ba.
Hukumar dillacin labarai na kasa, ta ce Bumi Adeyemo da Abiola Adeyemo na jam’iyyun APM da APP sun gamsu da Tinubu a matsayin wanda za a zaba.
Karbar katin zabe
Ku na da labari cewa fiye da 98% na mutanen jihohin Bauchi, Anambra da kuma Katsina da aka yi wa rajistar PVC, sun karbi katin zabensu kafin a rufe kofar.
Jihohin da jama’a suka fi yin wasa da karbar katin yin zaben sun hada da Oyo, Ogun da Legas. Duka jihohin su na Tiniubu na yankin Kudu maso yamma ne.
Asali: Legit.ng