Daruruwan Mambobin Jam'iyyun PDP da LP Sun Koma APC a Abuja
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ya samu wani babban tagomashi ana dab da zaɓe
- Ɗaruruwan mambobin jam'iyyun PDP da LP sun koma bayan tafiyar sa a birnin tarayya Abuja
- Mambobin sun bayyana dalilan da ya sanya suka zaɓi komawa bayan Tinubu da Shettima
Abuja- Ana saura ƙasa da kwana biyu a fara zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya, jam'iyyun PDP da Labour Party sun rasa ɗumbin mambobin su a birnin tarayya Abuja.
Tuni har jam'iyyar APC ta karɓi mambobin jam'iyyun masu sauya sheƙa zuwa cikinta a ranar Laraba. Rahoton Punch
Kodinetan wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu mai suna National Mass Movement for Better Orientation ta ƙasa, Dr Hawa Iyatu-Bagu, ta bayyana cewa sauya sheƙar tasu wata alama ce dake nuni da cewa APC zata yi nasara a zaɓen ranar Asabar.
Iyatu-Bagu tace ƙungiyar ta daɗe tana tattaunawa da masu sauya sheƙar inda take cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
”Yau waɗanda suka karɓi gaskiya sun yanke shawarar bin tawagar da zata yi nasara."
“Mun bi lungu da saƙo muna neman ƙuri'u sannan mafi yawan su dake a wannan wajen shugabanni ne domin idan da dukkanin su ne za su zo to wajen nan yayi mana kaɗan."
“Saboda haka, sai muka nemi shugabannin su da su zo su gayawa duniya cewa sun fice daga jam'iyyun PDP da LP, sannan su bayyana shirin su na yiwa Tinubu da Shettima ruwan ƙuri'u."
Dalilin Su Na Komawa APC
Tun da farko, Mr Titus Musa, tsohon shugaban matasan jam'iyyar PDP na mazaɓar Gwarinpa, ƙaramar hukumar Abuja Municipal, shine ya jagoranci sauran mambobin.
Tsohon shugaban ya bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne domin su zaɓi Bola Tinubu. Rahoton Within Nigeria
”Saboda tarihin da yake da shi na yin nagartattun ayyuka a jihar Legas da kuma gudunmawar sa wajen cigaban ƙasa."
”Muna da tabbacin cewa shirin da APC take da shi mai kyau ne sannan Tinubu yana da cigaban da zai kawo wa Najeriya." A cewar sa
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace jam'iyyar zata lashe zaɓen ranar Asabar.
Shugaban ya bayyana dalilan da suka sanya yake jin cewa jam'iyyar APC ce zata yi nasara a zaɓen.
Asali: Legit.ng