Kwankwaso, Atiku, Tinubu Ko Obi: Manyan Sarakunan Yarbawa 7 Sun Fito Karara Sun Bayyana Dan Takarsu A 2023

Kwankwaso, Atiku, Tinubu Ko Obi: Manyan Sarakunan Yarbawa 7 Sun Fito Karara Sun Bayyana Dan Takarsu A 2023

  • Kwana biyu kafin zaben shugaban kasa na 2023, sarakunan gargajiya daga kudu maso yamma da karin jihohi biyu, Kwara da Kogi, sun fitar da dan takarar da su ke goyon baya
  • Sarakunan sun bayyana goyon bayan su ga dan takarar shugabancin kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • A wata sanarwa da suka fitar bayan tattaunawar da su ka gudanar, sarakunan sun ce tarihin ayyukan da Tinubu yayi a baya ne ya sa suka zabe shi akan sauran yan takarar

Ibadan, Jihar Oyo - Gamayyar sarakunan Yarabawa sun hada kai tare da goyon bayan dan takarar shugabancin kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a cigaba da shirin zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga Fabrairu.

Sarakunan Yarabawan da suka fito daga jihohin Ekiti, Lagos, Kogi, Kwara, Ogun, Ondo, Osun, da kuma Oyo, sun bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da suka fitar bayan tattaunawar da su ka gudanar a dakin taro na International Conference Centre, da ke jami'ar Ibadan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Malaman Kano Sun Bayyana Dan Takarar Da Za Su Zaba Tsakanin Atiku Da Tinubu

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023 da Ooni na Ife. Hoto: KOLA SULAIMON/AFP, PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Source: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ooni na Ife da sauran sarakunan Yarabawa suna fatan ganin Bola Tinubu ya gaji kujerar shugabancin kasa.

Legit.ng ta ruwaito cewa sarakunan sun gamsu da manufofin da Tinubu ya gabatar a lokacin tattaunawar. Kusan gaba daya sarakunan kasar Yarabawa, Kwara da Kogi gaba daya sun amince da takarar tsohon gwamnan na Jihar Lagos.

Shugabancin kasa na 2023: Abin da yasa muka goyi bayan Tinubu - Sarakunan Yarbawa

Sarakunan Yarabawan sun amince da cewa Tinubu ya fi duk sauran cancanta da ya gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya.

Sarakunan sun gamsu da Tinubu ''da irin gudunmawar da ya bawa dimukradiyya da kuma irin rawar da ya taka don cigaban dimukradiyya a Najeriya.''

Wani sashi na labarin ya bayyana cewa:

''Abu ne a bayyane muna goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu saboda irin kyakkyawan tarihi da kuma irin muhimman abubuwan da ya cimma wanda ya sa ya hau saman sauran yan takarar a matsayin wanda kadai zai iya kawa hadin kai, daidaito da adalci ga tsarin Najeriya."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ta Cika Da Atiku Yayin da Jam’iyyun Adawa 5 Suka Marawa Tinubu Baya a Jihar Da PDP Ke Iko

Kiristoci sun yi addu'a ta musamman don nasarar Bola Tinubu a zaben 2023

A wani rahoton, al'umma mabiya addinin kirista a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya sun taru sun yi addu'a ta musamman don nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a zaben 2023.

An yi taron ne a otel din Illaja da ke Akanran a garin Ibadan a jihar Oyo kuma ya samu halarcin a kalla kungiyoyin kirista guda 1000 kamar yadda The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164