"Mun Lamuncewa Atiku Don Goyon Bayan Tikitin Musulmi Da Kirista" – Malaman Kano

"Mun Lamuncewa Atiku Don Goyon Bayan Tikitin Musulmi Da Kirista" – Malaman Kano

  • Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa, kungiyar malaman Kano sun bayyana matsayinsu kan wanda za su zaba
  • Kungiyar Malaman Kano sun ayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar na PDP saboda tikitin Musulmi da Kirista
  • A ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da babban zaben shugaban kasa

Kano - Kungiyar malaman Musulunci a jihar Kano sun ayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar.

Sun lamuncewa Atiku ne saboda goyon bayan tikitin Musulmi da kirista bisa ga tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, rahoton Leadership..

Okowa da Atiku a tsaye suna jawabi
"Mun Lamuncewa Atiku Don Goyon Bayan Tikitin Musulmi Da Kirista" – Malaman Kano Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Dalilinmu na goyon bayan Atiku, Malaman Kano

Da yake fitowa daga wani taro a Kano a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Sheikh Adam Koki, ya fada ma manema labarai cewa sun ji dadin yadda Atiku ke mutunta yanayin kasar mai addinai da yawa, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

"Ka Janye Wa Kwankwaso", Wasu Kungiyoyi Suka Roki Atiku Kwanaki Kadan Kafin Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman wadanda suke ganin hadin kai a matsayin abu mai matukar muhimmanci sun kuma bayyana ware wani sashi na kasar a matsayin aikin cin amana.

Ya ce sun yi nazari sosai a kan dukkanin yan takarar sannan suka cimma matsaya cewa Atiku ne ya fi cancanta.

Hazalika kungiyar ta ce dan takarar na PDP yana da gogewar da zai iya fitar da Najeriya daga wannan kangin da take ciki kasancewar ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa a baya.

Ya ce:

"Dalilinmu na goyawa Atiku Abubakar baya shine cewa yana da tarin gogewa kasancewar ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa a baya kuma yana da ikon da zai iya gyara Najeriya duba da halin da ake ciki a yanzu.
"Mu da mabiyanmu za mu zabi Atiku kuma a cikinmu akwai malamai daga bangarorin Tijjaniyya, Izala, Qadiriya da ma shugabannin Musulunci da yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ta Cika Da Atiku Yayin da Jam’iyyun Adawa 5 Suka Marawa Tinubu Baya a Jihar Da PDP Ke Iko

"Muna ganin wannan a matsayin dama ce ta ceto Najeriya daga rikicin addini da rashin hadin kai kamar yadda yake a tikitin Musulmi da Musulmi."

Sai dai kuma, ya yi bayanin cewa kungiyar bata yanke shawara kan goyon bayan kowani dan takarar gwamna ba a Kano domin gudun sabani da rashin amince.

Ya kara da cewa:

"Kowa na da ikon goyon bayan zabinsa a matsayin gwamnan Kano."

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyun adawa guda biyar a jihar Oyo sun ayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng