APC, PDP da NNPP Zasu Gudanar da Babban Yaƙin Neman Zaɓe a Wuri Guda Yau a Kano - Ku Hakura Inji ƴan Sanda

APC, PDP da NNPP Zasu Gudanar da Babban Yaƙin Neman Zaɓe a Wuri Guda Yau a Kano - Ku Hakura Inji ƴan Sanda

  • Hukumar ta Yan Sandan Jihar Kano Tace ta Samu Saƙon Bukatar Sahalewa Domin Gudanar da Tarukan Kamfen Guda Uku Rigis a Waje Guda.
  • Duba da Yanayin Tasirin Jam'iyyun, APC, PDP, da NNPP Hukumar Yan Sanda ta buƙaci su Hakura Domin Gudun Ɓarkewar Rikici.
  • Bayan dogon zama da aka yi, an Kasa Samun Matsaya Domin Jam'iyyun Sun Turje Cewa Lallai Zasu Gudanar da Taron su a Yau.

Kano - A yau ne za'a yi wani salon siyasa mai sarƙaƙiya a jihar Kano a siyasance, inda jam'iyyun PDP, APC da NNPP zasu gudanar da yaƙin neman zaɓen su na ƙarshe a cikin ƙwaryar garin Kano a waje mara nisa da juna.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake daf da ƙara tunkarar zaɓukan ƙasa, inda al'amuran siyasa ke ta ƙara kankama gadan-gadan.

Kara karanta wannan

"Mun Gano Su" Jam'iyyar PDP Ta Fallasa Shirin El-Rufa'i Na Siyan Ƙuri'a a jihar Kaduna

Kwankwaso
Kwankwaso da Ganduje Sun yi mulki
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaƙin neman zaɓen, masana na kallon sa a matsayin wani takun ƙarshe. Yaƙin ƙarshe da ka iya zama zakaran gwajin dafi wajen nuna yadda kowacce jam'iyya keda tasiri a Kano.

Bugu da ƙari, ana ganin ka iya zuwa yabar baya da ƙura. Idan akayi la'akari da yadda lamurra suke gudana na zaman ɗarɗar a siyasance a tsakanin jam'iyyun.

Tunda fari dai, hukumar ƴan sanda ta jihar Kano ce ta samu saƙonnin neman sahalewar gudanar da yaƙin neman zaɓen.

Inda ta gano cewar, za'a gudanar da tarukan ne a wuri guda kuma ranar Alhamis ɗin nan biyo bayan neman izini da kowacce jam'iyya tayi wajen hukumar.

Hukumar Yan Sanda ta Danni Kirjin Yan Siyasar

Hakan ne yasa hukumar ƴan sandan ta ƙasa reshen jihar Kano batayi wata wata ba tayi ta maza. Domin roƙon jam'iyyun su haƙura da gudanar da taron duk domin kawo maslaha ga zaman lafiyan da ake riritawa.

Kara karanta wannan

Abu Ɗaya Ne Tak, Abinda Inyamurai Zasu Yi Domin Samun Shugabancin Najeriya, Sanatan APC

Batun dannar ƙirjin ta fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar SP Haruna Kiyawa a safiyar Alhamis ɗin nan kamar yadda Freedom radiyo ta ruwaito.

A cewar sa:

"Akwai jam'iyyu guda uku, NNPP, PDP, APC, sun sanar da rundunar ƴan sandan jihar Kano cewa zasu gudanar da jerin gwano na yaƙin neman zaɓe ranar Alhamis 23 ga watan 2, na wannan shekara ta 2023 a cikin ƙwaryar birnin Kano.
"Ganin cewa wuraren da zasu gudanar da tarukan suna kusa da juna, wanda haka zai iya haifar da matsalar tsaro, wannan ce tasa mai girma kwamishinan ƴan sanda CP Muhammad Yakubu ya gayyaci wakilan waɗannan jam'iyyu. Inji shi.

SP Kiyawa yaci gaba da cewa:

"Bayan dogon zama da aka yi, an kasa samun matsaya, hakazalika Kwamishinan yan sanda ya roƙe su dasu duba zaman lafiyan da muke dashi a Kano amma abin yaci tura.
"Hakane tasa rundunar yan sanda ta jihar Kano, ta basu shawara cewa duk jam'iyyun su ɗaga wannan gangami zuwa bayan zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisar tarayya , wanda za'ai ranar 25 ga watan 2 na wannan shakara ta 2023."

Kara karanta wannan

Babban Dalili Ɗaya Rak Da Ya Sanya Ƴan Najeriya Ba Zasu Zaɓi Tinubu Ba, Datti Baba-Ahmed

Siyasar jihar Kano

Jihar Kano dai, tayi ƙaurin suna wajen siyasa, domin gida ne ga ɗan takarar shugaban ƙasa a tsagin jam'iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Tsohon Mininistan ilimi Malam Ibrahim Shekarau, da Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ke mulki a jihar yanzu haka.

Inda tsagin gwamnati ke marawa Dr. Nasir Yusif Gawuna baya, Rabi'u Musa Kwankwaso ke marawa Abba Kabir Yusif baya, a yayin da ɓangaren PDP na Malam Ibrahim Shekarau ke goyawa Muhammad Abacha.

Duk da kujerar nayin kwan gaba kwan baya na ɗan takarar PDP akan waye zai gaji kujera mafi girma a jihar.

Abin jira a gani, ko zasu gudanar da taron kamar yadda suka tsara ko sun ɗauki shawarar ta ƴan sandan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida