"Ka Janye Wa Kwankwaso", Wasu Kungiyoyi Suka Roki Atiku Kwanaki Kadan Kafin Zabe

"Ka Janye Wa Kwankwaso", Wasu Kungiyoyi Suka Roki Atiku Kwanaki Kadan Kafin Zabe

  • Wasu gamayyar kungiyoyin wayar da kan jama'a sun bukaci Atiku Abubakar da ya janyewa Kwankwaso takarar shugabancin kasa
  • Shugaban kungiyar ya ce Najeriya ta na bukatar mai hangen nesa irin na Kwankwaso da kuma gogewa don ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki
  • Kungiyoyin sun bayyana cewa al'ummar karkara ne su ka nemi da su yi kira da Atiku Abubakar ya janye takarar don gudun kada a karkasa kuri'u a Arewa

Abuja - Gamayyar kungiyoyin wayar da kan jama'a a ranar Laraba ta yi kira ga dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya janyewa dan takarar jam'iyyar NNPP, Musa Kwankwaso, don gudun kada a kacaccala kuri'un Arewa.

Kungiyoyin, sun ce, Atiku ya yi iya bakin kokarin sa lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa, jaridar The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku, Tinubu Da Wasu Yan Takara Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Rabiu Kwankwaso
Kungiya ta yi kira ga Atiku ya janye wa Kwankwaso. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke zantawa yan jarida a Abuja a sakateriyar jam'iyyar NNPP, shugaban gamayyar kungiyoyin, Bishop Godwin Abah, ya ce Najeriya tana mawuyacin hali saboda haka, akwai bukatar gogewar siyasa da kuma jagoranci irin na Kwankwaso don shugabantar kasar nan.

Abah ya ce kungiyoyin sun tantance manyan jam'iyyu da yan takarar su, tare da manufofinsu da kuma abubuwan da suka cimma, daga karshe su ka yanke shawarar Kwankwaso yafi sauran yan takarar cancanta.

Ya ce:

''Jajirtaccen jagora mai tarin mutunci, Kwankwaso ya bunkasa Kano a matsayin gwamnan jihar har karo biyu ga karin sanin makamar aiki a matsayin tsohon ministan tsaro, jakada, sanata, mataimakin kakakin majalisar wakilai, tsohon dan majalisa da sauransu, don iya gudanar da Najeriya a matsayin shugaban kasa.
''Kuma ra'ayin mutanen karkara ne a fadin kasar nan su ka ce mu roki Alhaji Atiku Abubakar da ya janye takara don marawa kwararre, gogagge, mai koshin lafiya kuma mai sanin makama Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Dab da zabe, Tinubu ya dura a jiharsu, zai yi wani taro da shugabannin Yarbawa

''Sannan, kungiyoyin sun yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar PDP da ya janyewa dan takarar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso don kada a karkasa kuri'u a Arewa."

Ya cigaba da cewa:

''Kwankwaso zai kawo sabbin tsare-tsare a gwamnati, ya dawo da martabar baudaddiyar kasar da ta fi ganin illoli sama da yadda ta more dimukradiyya ya kuma gina sabuwar Najeriya irin wadda mu ke bukata.
''Atiku yayi iya bakin kokari ga kasar nan, muna godiya da abubuwan yayi a matsayin mataimakin shugaban kasa. Yana nan a matsayin dattijon kasa.
''A yau, kasar nan tana cikin matsala, kaddarar Najeriya tana tangal-tangal kuma akwai bukatar kwarewar siyasa, karfin iko, tunani da hangen nesa irin Kwankwaso - Isaac Idahosa don su jagoranci kasa su kuma ceto kasar nan daga tabewa.''

"Ban karbi kudi daga hannun Tinubu ba": Jarumar fina-finai ta mayarwa masu sukarta martani

Jarumar fina-finan Nollywood, Toyin Abraham ta ce ba don kudi ta ke goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar jam'iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

Saura kwana 5: Kungiyar Arewa ta AFC ta fadi dan takarar da take so ya gaji Buhari

Ta ce tsinuwar da wasu ke mata ba zai kama ta ba saboda ba kudi yasa ta ke son Tinubun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164