Babban Gangamin Legas: Da Daske Tinubu Ya Watsa Wa Mutane Sabbin Kudi, APC Ta Fayyace Gaskiya

Babban Gangamin Legas: Da Daske Tinubu Ya Watsa Wa Mutane Sabbin Kudi, APC Ta Fayyace Gaskiya

  • Jam'iyyar APC ta karyata rahoton da ya bayyana dan takararta, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya watsa kudi ga taruwar jama'a a Lagos
  • Seye Oladejo, mai magana da yawun APC reshen Jihar Lagos, ya ce yan adawa ne suka shirya hakan
  • Oladejo ya kara da cewa an kirkiri rahoton don bata Tinubu a idon yan Najeriya wanda ke shan wahala saboda chanjin kudi

Legas, Najeriya - Jam'iyyar APC reshen Jihar Lagos ta yi watsi da rahoton da ke cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya watsa wa mutane sabbin kudade a wurin taro a ranar Talata, 21 ga Fabrairu.

Tinubu yana Lagos don rufe yakin neman zabe da ya gudana a filin wasa na Teslim Balogun, Surulere, Legas.

Gangamin Bola Tinubu
Hotunan taron gangamin Asiwaju Bola Tinubu a Legas. Hoto: @BashirAhmaad, @officialSKSM
Asali: Twitter

A wata sanarwa da aka aikowa Legit.ng ta bakin mai magana da yawunta Seye Oladejo, jam'iyyar APC reshen Jihar Lagos ta ce batun Tinubu ya watsa kudi a taron ba komai ba ''face karya daga wajen mutanen banza''.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tsohon Minista Ya Bayyana Yankin Da Atiku Zai Lashe

Oladejo ya ce rahoton daukar nauyin ''bata garin yan adawar siyasa ne''.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

''A wani rahoto da ke yawo a halin yanzu, ya bayyana yadda Asiwaju Tinubu ya ke watsa damin kudade ga taruwar mutane a Oshodi yayin da tawagarsa ke wucewa daga filin jirgin saman Lagos zuwa filin wasa na Teslim Balogun, Surulere, Lagos,'' kamar yadda wani bangaren sanarwar ya shaida.

Shiri ne don cutar da takarar Tinubu - APC Legas

Jam'iyyar APC reshen Jihar Lagos ta kara da cewa rahoton ''bangare ne na irin mummunan shirin da ake yi don bata Tinubu a idon miliyoyin yan Najeriya da suka samun kudaden da ke ajiye a banki da suka sha wahalar tarawa.''

Sanarwar ta cigaba da cewa:

''Asiwaju ya damu da halin kuncin da yan Najeriya su ka shiga na rashin amfanar kudaden su saboda rashin wadatuwar sabon kudi daga CBN. To, a ina Asiwaju ya ga sabon kudin da zai watsa a titunan Lagos?

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Dab da zabe, Tinubu ya dura a jiharsu, zai yi wani taro da shugabannin Yarbawa

''In da mun yi niyya, za mu iya yin shiru akan wannan karya amma saboda yadda ta yadu (daya daga cikin wanda aka hayo yan adawa yanzu sun shiga damuwa da nasarar APC ranar 25 ga Fabrairu). Amma mun yanke shawarar yin wannan karamar sanarwar saboda wanda za su iya yadda da wannan karya.
''Idan aka yi kallo na tsanaki cikin bidiyo(da ke hade da rahoton karyar) za a iya ganin shugabannin APC biyu daya ya na jefa hulunan fez caps da takardun yakin neman zabe ga jama'a. Tabbas ba kudi ba. Jam'iyyar, saboda haka, tana kira da magoya baya da sauran yan Najeriya da su kwantar da hankali kuma su zabi Tinubu da jam'iyyar APC ranar Asabar, 25 ga Fabrairu."

Orji Kalu ya ce sauya tsarin kudi ba zai hana Tinubu cin zabe ba

A wani rahoto, kun ji cewa bulaliyar jam'iyyar tarayya, Sanata Orji Kalu ya ce tsarin sauya takardun naira da babban bankin kasa, CBN, ta yi ba zai shafi nasarar Bola Tinuba.

Kara karanta wannan

Rikici: Saura kwana 6 zabe, an harbe jigon APC a wurin taron kamfen a wata jihar PDP

Kalu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya aka yi da shi a Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel