Zaben Ranar Asabar: Shugaban INEC Ya Gana Da Buhari a Villa

Zaben Ranar Asabar: Shugaban INEC Ya Gana Da Buhari a Villa

  • Yan kwanaki kafin babban zaben Najeriya, an yi wata ganawa mai muhimmanci tsakanin Shugaba Buhari da shugaban hukumar INEC
  • Farfesa Mahmoud Yakubu ya ziyarci shugaban kasar a villa don tsara yadda za a gudanar da zabe cikin nasara
  • A ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne za a yi zaben shugaban kasa inda za a fitar da magajin Shugaba Buhari

Abuja - Gabannin zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya da za a yi a ranar Asabar mai zuwa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Farfesa Mahmoud Yakubu ya korowa shugaban kasar jawabai kan tsare-tsarensu a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasa Buhari a tsaye da takarda a hannunsa
Zaben Ranar Asabar: Shugaban INEC Ya Gana Da Buhari a Villa Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya yi bayanin cewa ganawar tasu na daga cikin kokarin da suke yi na ganin cewa zaben ya gudana cikin nasara, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Shirin Zabe Na Ta Kankama, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Rarraba Muhimman Kayan Aikin Zabe

Dole mu tabbatar da ganin an yi zabe cikin nasara, Buhari

Buhari ya ambaci batun ganawa da shugaban na INEC ne yayin da yake bayani kan dalilinsa na yin lattin zuwa wajen kaddamarwa da milka kayan tsaro da ya kai sama da biliyan 12 ga rundunar soji da na yan sandan Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, hukumar zabe ce ta dakatar da shi na tsawon mintoci biyar din da ya ajiye kungiyar ta CACOVID tana jira yana mai tunatar da kowa cewa ya zama dole ayi duk mai yiwuwa don yin zabe cikin nasara, rahoton Daily Trust.

Buhari ya sanar da bakin nasa:

"INEC ce ta tsayar da ni. Kun san Asabar mai zuwa babban rana ce a garemu kuma ina karbar umurni daga INEC don na tabbatar da ganin cewa babu wani uzuri wajen yin zaben cikin nasara."

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Yi Sabon Jawabi Ana Kwana 4 Zabe

Hukumar INEC ta fara rabon muhimman kayan zabe

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara rabon kayan zabe masu muhimmanci a ofishoshinta da ke kananan hukumomin jihar Cross River.

An yi rabon kayayyakin ne a gaban jami'an hukumomin tsaro daban-daban, jam'iyyun siyasa da kuma kungiyoyin jama'a a kokarin INEC na kore shakku ko zargi daga zukatan wadanda abun ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng