Jerin Sunayen Attajiran Dake Siyasa a Zaɓen 2023 na Najeriya
- Najeriya na dab da zaɓen shugabannin da za su cigaba da jan ragamar ƙasar nan a zaɓen dake tafe
- Daga cikin ƴan takarar dake neman muƙamai daban-daban, akwai hamshaƙan attajirai
- Hamshaƙan attajirai da dama na fafata takara ko goyon bayan wasu ƴan takara a babban zaɓen 2023
A yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, ɗaruruwan ƴan siyasa zasu fafata a takarar neman kujeru daban-daban.
Da yawa daga cikin su hamshaƙan attajirai ne waɗanda yanzu suka tsunduma cikin harkar siyasa, ta hanyar tsayawa takara ko marawa wani ɗan takara baya.
Ga jerin hamshaƙan attajiran da ake damawa da su a zaɓen 2023:
1. Bola Ahmed
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tinubu Bola Tinubu tsohon sanata ne kuma tsohon gwamnan jihar Legas tun daga 1999 zuwa 2007. Tinubu yana da harkokin kasuwanci da dama tun daga ɓangaren man fetur da iskar gas, jarida da hannun jari a kasuwanci da dama.
Yanzu shine ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
2. Atiku Abubakar
Atiku Abubakar tsohon gwamnan jihar Adamawa ne kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin Obasanjo tun daga 1999 har zuwa 2007.
Kafin ya shiga siyasa Atiku Abubakar yayi aiki da hukumar kwastam har na tsawon shekara 20. Bayan ya bar aikin kwastam ya kafa kamfanin INTELS.
Atiku wanda yake takarar shugabam ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, yana da harkokin kasuwanci da dama.
3. Peter Obi
Peter Obi yayi gwamnan jihar Anambra tun daga shekarar 2007 zuwa 2014. Kafin shigar sa siyasa, Obi yana da harkokin kasuwanci da dama da yake yi kama daga banki, shigo da kaya da ƙere-ƙere.
Peter Obi yanzu shine ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party.
4. Ifeanyi Ubah
Ifeanyi Ubah hamshaƙin ɗan kasuwa ne daga jihar Anambra. Shine sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya.
Ya fara kasuwanci da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje kafin ya kafa manyan kamfanoni a ƙasar nan.
Shine ya kafa kamfanin Capital Oil and Gas, jaridar Authority Newspaper da kulob ɗin ƙwallon ƙafa na Ifeanyi Ubah Footbal Club.
5. Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka fi kowa shahara a yankin Kudu maso Gabas.
Yayi gwamnan jihar Abia har sau biyu sannan yayi sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.
Kalu yana da harkokin kasuwanci da dama tun daga kan fannin sufurin jiragen sama, man fetur da iskar gas, banki, jarida da wasanni.
6. Tonye Cole
Tonye Cole shahararren ɗan kasuwa ne wanda aka kafa kamfanin Sahara Group da shi.
Bayan yayi rashin nasarar yin takarar gwamnan jihar Rivers a shekarar 2018, Cole shine ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen 2023 na gwamnan jihar.
Jerin Sunayen Ƴan Takarar Da Suka Mutu Ana Gab Da Zaɓen 2023
A wani rahoton kuma, ƴan siyasa da dama dake takara a zaɓen 2023 sun rigamu gidan gaskiya dab da a fara zaɓen.
Mun tattaro muku jerin wasu mutum 10 daga cikin su.
Asali: Legit.ng