2023: Atiku Bai Kai Matsayin Samun Kuri'un Mutanen Ribas Ba, Wike

2023: Atiku Bai Kai Matsayin Samun Kuri'un Mutanen Ribas Ba, Wike

  • Gwamna Wike ya maida martani ga Atiku kan kiran wasu tsirarun mutanen Ribas ya gana da su a Abuja
  • Wike, jagoran gwamnonin G-5, ya ce ko kaɗan Atiku bai cancanci kuri'un mutanen jiharsa ba domin ya ci masu mutunci
  • Ya ce sun shirya tsaf domin koyawa wasu mutane hankali a zaɓen ranar Asabar mai zuwa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya caccaki ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, kan gudanar da taron al'umma na Ribas a Abuja.

Jaridar The Nation ta rahoto gwamna Wike na cewa tsohon mataimakin shugaban kasan bai cancanci ko kuri'a ɗaya daga jihar Ribas ba.

Gwamna Wike.
2023: Atiku Bai Kai Matsayin Samun Kuri'un Mutanen Ribas Ba, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Ya ce wannan abun da Atiku ya yi cin mutunci ne da ƙasƙanci ga jihar kuma ya yi mamakin meyasa har yanzun ɗan takarar ke son mutanen Ribas su zaɓe shi ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Tinubu Ya Yiwa Borno Lokacin Boko Haram da Babu Wanda Ya Taɓa Mana, Gwamna Zulum

Wike ya bayyana cewa masu katin zaɓe a jihar zasu fita su dangwalawa ɗan takaran da kowa ya aminta da cewa zai iya haɗa kan Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da fara aikin faɗaɗa titin Emohua zuwa Abalama/Tema Junction, karamar hukumar Emohua.

Ya jaddada cewa babu wani mai tsaurin idon da zai dakatar da masu kaɗa kuri'un Ribas daga zaben ɗan takarar shugaban kasan da ya kwanta masu a rai.

A cewarsa, mutanen da Atiku ya gayyata suka saurari jawabinsa a Abuja ba jinin Ribas bane, idan kuma suna da ja su dawo gida su saurari ɗan takarar da ya dace.

Gwamnan ya ce:

"Ka kira mutanen Ribas su same ka a Abuja ku tattauna, wannan ba cin mutunci bane? Ba zaka iya zuwa Ribas ka tattauna damu ba, kana nufin Ribas ba tsaro amma kana bukatar kuri'unsu."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Zai Girgiza da Sakamakon Zabe a Arewa Maso Yamma, Jigo Ya Fasa Kwai

"Mutanen da suka nuna baku da zaman lafiya kuma su ke neman ku zaɓe su, abun da takaici domin babu wani mai hankali da zai ɗauki wannan cin mutuncin."

Bugu da kari, Wike ya jaddada cewa sun shirya wa zaben ranar Asabar kuma zasu koya wa wasu mutane hankali, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yan takarar gwamna 3 sun sauya sheƙa

A wani labarin kuma Yan Takarar Gwamnan Kano Uku Sun Janye, Sun Koma Bayan Sha'aban Sharada

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano karƙashin inuwar jam'iyyar ADP, Sha'aban Ibrahim Sharada, ya kara samun babban goyon bayan makonni kafin zaɓe.

Masu neman zama gwamnan Kano daga jam'iyyu uku da ɗan takarar mataimaki na APGA sun janye daga takara, sun ce Sharada ya dace da Kano a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262