Saura Mako Ɗaya Zabe, Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Jam'iyyar PDP a Ondo

Saura Mako Ɗaya Zabe, Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Jam'iyyar PDP a Ondo

  • Yayin da ya rage saura mako ɗaya babban zabe, jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin yan takarar majalisar tarayya a Ondo
  • Babbar Kotun tarayyya mai zama a Akure ta kori ɗan takarar jam'iyyar APC na mazaɓar Akoko a zaben 2023 mai zuwa
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu, watau nan da mako ɗaya INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya

Ondo - Babbar Kotun tarayya mai zama a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta soke tikitin ɗan takarar majalisar tarayya na jam'iyyar APC a mazaɓar Akoko ta Kudu-gabas/Kudu-yamma, Mr. Gboyega Adefarati.

Kotun ta ayyana zaben fidda gwanin da ya samar da ɗan takarar a matsayin haramtacce wanda ya saɓa wa tsari, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Tutar APC.
Saura Mako Ɗaya Zabe, Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Jam'iyyar PDP a Ondo Hoto: APC
Asali: Facebook

Ɗaya daga cikin waɗanda suka fafata a zaben, Segun Ategbole, ne ya garzaya gaban Kotun inda ya zargi an saɓa doka da zalunci kana ya nemi Alkali a ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takara.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kara Shiga Tasku, Gwamnan PDP Ya Yanke Shawara Ta Karshe Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a 2023

Kotun, a hukuncin da mai shari'a T.B Adegoke, ya yanke, ya ce ba zai yuwu APC ta ɗora wani abu akan wurin da bakomai kuma ta yi tsammanin abun ya tsaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta da ɗan takarar majalisar tarayya a wannan mazaɓa a zaɓe mai zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 saboda ba ta gudanar da halastaccen zaɓe ba.

Bugu da ƙari, Kotun ta haramtawa jam'iyyar APC gudanar da sabon zaɓen fidda gwani domin lokaci ya riga da ya ƙure, domin hukuncin ya zo ƙasa da kwanaki 180 da kundin dokokin zaɓe 2022 ya ba da dama.

Daga nan Kotun ta umarci INEC karta karɓi sunan wannan ɗan takara ko wani daban daga jam'iyyar APC kuma ta haramtawa Mista Adefarati ci gaba da ayyana kansa a matsayin ɗan takara.

Kara karanta wannan

Bayan Wike, Bola Tinubu Ya Lallaɓa Wurin Wani Gwamnan PDP Ana Dab da Zaɓen 2023

APC ta maida martani

Yayin da take maida martani kan hukuncin Kotun, jam'iyyar APC a Ondo, ta yi fatali da hukuncin kana ta sha alwashin ɗaukaka ƙara a Kotun gaba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Alex Kalejaye, ya fitar, ya ce APC ta samu koma baya sakamakon hukuncin domin ya shafi ɗan takararta na mazaɓar tarayya.

Kalejaye ya ce:

"Shugaban jam'iyya na jiha, Ade Adetimehin, ya tabbatar wa magoya bayan APC cewa zamu kalubalanci hukuncin a Kotun ɗaukaka ƙara, muna fatan samun nasara."

A wani labarin kuma Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Gwamnan jihar Benuwai ya tabbatar da cewa yana nan tare da tawagar G-5 amma ya zai yi wa Peter Obi aiki a zaɓen shugaban ƙasa.

Samuel Ortom ya bukaci matasa da su tashi tsaye su yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar LP a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Ya Cinyemun Kuɗi Kuma Ya Ƙi Zaɓena Zai Sheƙa Barzahu, Ɗan Takarar PDP a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262