El-Rufai: Yadda Yan Takarar Shugaban Ƙasa 2 Suka Samu Ɗaruruwan Sabbin Miliyoyin Takardun Naira
- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna Kaduna ya ce ba don dakile siyan kuri'u aka sauya fasalin naira ba
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce sauya fasalin kudin ya taimaka wurin rage tasirin kudi a siyasar kasar
- Amma, gwamnan na Jihar Kaduna ya ce yan takarar shugaban kasa 2 da abokin takara suna da sabbin miliyoyin naira saboda suna da hanya a wasu bankuna
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya cigaba da sukar tsarin sauya fasalin naira na babban bankin kasa, CBN.
A jawabin da ya yi wa jiharsa a Kaduna a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, Gwamna El-Rufai ya ce ba a ci nasarar manufar hana siyar kuri'a da aka ce don ita aka kawo tsarin ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan za a iya tunawa Shugaba Muhammad Buhari a jawabin da ya yi kasa ya ce ya san cewa sabon tsarin kudin zai taimaka wurin rage matsalar siyan kuri'u a babban zaben 2023.
Shugaban kasar ya ce:
"Na san wannan sabon tsarin kudin zai taimaka sosai wurin rage tasirin kudi a siyasa."
Sauya nairan bai shafi yan siyasa da aka yi don su ba, El-Rufai
Amma, Gwamna El-Rufai ya ce tsarin bai shafi yan siyasan da CBN ta gamsar da Buhari cewa zai taba su ba.
Gwamnan na Kaduna ya ce yan takarar shugaban kasa biyu da wani dan takarar mataimakin shugaban kasa daga jam'iyyun adawa sun mallaki ko suna da alaka mai kyau da wasu manyan bankuna a kasar.
Ya kara da cewa yan takarar da ya ke nufi suna da daruruwan miliyoyi na sabbin takardun nairan amma yan kasuwa, dalibai, manoma da sauran yan kasa suna wahalar cire tsirarun dubban naira don cin abinci da kananan bukatu.
Kalamansa:
"Duk da haka, yan siyasar da aka gamsar da shugaban kasar cewa tsarin zai shafe su abin ma bai shafe su ba zuwa yanzu. Hakika, biyu cikin yan takarar shugaban kasa, da abokin dan takara na jam'iyyun adawa sun mallaki bankuna ko suna da hanyar samun kudade daga bankuna masu lasisi.
"Don wannan dalilin da wasu tsare-tsare, wadannan yan siyasan suna da daruruwan miliyoyi na sabbin kudin, yayin da yan kasuwa, tireda, dalibai da sauran yan kasa suna bin layi na kwanaki don cire tsirarun dubban naira don siyan abinci da abubuwar bukata."
El-Rufai ya ki bin umurnin Buhari kan hana amfani da tsaffin naira
A bangare guda, gwamnan na jihar Kaduna El-Rufai ya umurci mutanen jiharsa su cigaba da kashe tsaffin kudi yana mai cewa kotun koli ne kadai za ta yanke hukunci kan halascin kudin.
Asali: Legit.ng