Hana Amfani Da Tsaffin Naira: Abu 4 Da Ya Kamata Ku Sani Yayin Da Kotu Ta Ɗage Ƙarar Da Gwamnoni Suka Shigar
FCT Abuja - Yan Najeriya suna nan sun zuba wa kotun kolin Najeriya ido a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, domin su sani ko za su cigaba da kashe tsaffin takardun N200, N500 da N1000.
Idan za a iya tunawa wasu gwamnatocin jihohi sun maka gwamnatin tarayya kara a kotun koli suna neman a dakatar da aiwatar da dokar sauya fasalin takardun naira na babban bankin Najeriya, CBN.
Ranar 10 ga watan Fabrairu ne ranar da CBN ta ambata a matsayin ranar karshe na canja tsaffin naira don samun sabbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, jihohin sun yi nasara a kotun koli a ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, a yayin da kotun ta dakatar da CBN daga aiwatar da dena karbar tsaffin kudin a ranar 10 ga watan Fabrairu.
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
Kotun kolin ta sake sanar da cewa za ta saurari karar ne gwamnonin APCn suka shigar a ranar Laraba 15 ga watan Laraba.
Kamar yadda aka sanar, kotun ta zauna a ranar Laraba. Amma mai ya faru a kotun? Ga muhimman abubuwa hudu da ya kamata ka sani game da zaman kotun na baya-baya game da tsarin sauya fasalin naira.
1. Kotun kolin ta dage cigaba da sauraron karar
A ranar Laraba, kotun kolin da ke zamanta a Abuja ta sake dage cigaba da sauraron karar kan hana amfani da tsaffin takardun naira.
Sabon ranar da za a cigaba da sauraron karar shine ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu.
2. Har yanzu halas ne a kashe tsaffin naira
A wani sabon cigaba, jihohi tara sun shiga karar wacce da farko gwamnonin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara ne suka shigar.
Kotun kolin ta jadada halascin amfani da tsaffin takardun N200, N500 da N1000.
A cewar kotun kolin, har yanzu umurnin da ta bayar na dakatar da aiwatar da hana amfani da tsaffin takardun nairan a ranar 10 ga watan Fabrairu yana nan.
Kotun ta yi wannan karin hasken ne biyo bayan korafi da Abdulhakeem Mustapha (SAN), lauyan jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara ya yi.
Mustapha ya zargi FG da gwamnan CBN da rashin biyayya ga umurnin kotun kolin.
A martaninsa, Mai shari'a John Okoro wanda ya jagoranci zaman kotun kolin ya bukaci Mustapha ya shigar da korafinsa ta hanyar da ta dace.
A cewarsa, hakan zai bawa FG da damar yin martani.
3. Adadin jihohin da ke karar FG a kotu ya karu zuwa 10
A zaman kotun na ranar Laraba, an tabbatar cewa wasu jihohin baya ga Kaduna, Zamfara da Kogi suma sun yi karar FG.
A halin yanzu, jihohi 10 ne ke karar gwamnatin tarayya kan tsarin sauya fasalin nairan.
Jihohin sune Katsina, Legas, Cross Rivers, Ogun, Ekiti, Ondo da Sokoto, hakan na nufin wadanda suka yi karar zuwa 10.
4. Jihohi biyu sun nemi goyi bayan FG
A yayin da jihohi 10 ke karar gwamnatin tarayya kan sauya fasalin nairan, jihohi biyu, Edo da Bayelsa, sun goyi bayan gwamnatin tarayya.
Tawagar alkalan na kotun koli karkashin mai shari'a Okoro sun umurci jihohin biyu su daidaita kansu domin a saurari shari'arsu lokaci guda.
A baya mun kawo muku rahoton cewa akwai wasu jihohin Najeriya da kantina, yan kasuwa da bankuna ba su karbar tsaffin kudin duk da umurnin da kotun koli ta bada saboda a bangare guda CBN ta ce a dena karbar tsaffin takardun nairan.
A kan hakan ne wakilin Legit.ng Hausa ya nemi ji ta bakin wata lauya wacce ke aiki a jihar Kaduna. Lauyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce kotu ce ke yin fashin baki kan doka da ma'anatarta don haka ya kamata kowa a kasa ya bi umurnin kotu ba CBN.
Kalamanta:
"Bangaren shari'a ne ke da alhakin yin bayani kan doka da yadda za a aiwatar da ita, don haka ba a wannan lamarin ya kamata bankuna da sauran mutanen kasa su yi biyayya ga umurni ko hukunci da kotun koli ta yanke."
Asali: Legit.ng