Atiku Ya Yi Watsi da Mataimakin Gwamnan Enugu a Wurin Kamfen PDP

Atiku Ya Yi Watsi da Mataimakin Gwamnan Enugu a Wurin Kamfen PDP

  • Wani abun mamaki ya faru yayin da mataimakiyar gwamnan Enugu ta je wurin Atiku domin gaida shi a wurin kamfe
  • Wani mamban PDP ya bayyana cewa Misis Cecilia Ezeilo, ba ta nemi mutane su zaɓi Atiku ba a jawabinta kuma hakan bai masa daɗi ba
  • Misis Ezeilo ta je da nufin gaisawa da Atiku amma ya juyar da kai ba tare da miƙa mata hannu ba

Enugu - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Talata ya kunyata mataimakiyar gwamnan jihar Enugu, Cecilia Ezeilo.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wurin ralin kamfen shugaban ƙasa da ya gudana a jihar Enugu gabanin zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Ralin Enugu.
Atiku Ya Yi Watsi da Mataimakin Gwamnan Enugu a Wurin Kamfen PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Misis Ezeilo, mataimakiyar gwamna, ta nufi wurin da Atiku ke zaune domin su gaisa kuma su yi musabiha bayan ta gama jawabi ga dandazon magoya baya da suka halarci Ralin.

Kara karanta wannan

2023: Hantar Atiku Ta Kaɗa, Gwamna Wike Ya Faɗi Abinda Gwamnonin G-5 Zasu Yi Ranar Zaɓe

"Tun 1999 muke kan mulki kuma wannan lokacin ma ba zai zo da tasgaro ba, ina rokonku kamar yadda muka saba, to mu ɗora daga nan," Ezielo ta gayawa mahalarta ralin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan gama faɗin haka, ta sauko daga kan dandamalin kana ta nufi wurin da Atiku ya zauna ta miƙa masa hannu do nufin su gaisa amma ɗan takarar ya wayance kamar bai ganta ba.

Ganin haka, matainakiyar gwamnan ta koma wurin zamanta ba tare da ta gaisa da tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ko meyasa Atiku ya yi wa mataimakiyar gwamna haka?

Wani mamban PDP, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa ya ce bayan sabanin dake tsakanin Atiku da gwamnonin G5, wanda gwamnan Enugu ke ciki, akwai wani abu da ya faru a ralin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: DSS Ta Magantu Kan Titsiye Fani-Kayode, Tace Yanzu ta Fara

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban ƙasan bai ji daɗin yadda mataimakiyar gwamnan ta gaza rokon mazauna jihar su zaɓe shi a ranar 25 ga wata ba yayin jawabinta.

"Shin kunji a kalamanta ta nema wa Atiku kuri'u? Amsar ita ce a'a, kawai ta rinka wasa ne da kalmomi. Atiku ya yi tunanin tana goyon bayan Ubangidanta (gwamna Ugwuanyi)," inji shi.

A wani labarin kuma Atiku Ya Rikice, Ɗan Takarar Gwamna, Yan Takarar Sanatoci da Majalisun Tarayya Sun Koma APC

Jam'iyyar SDP ta rushe tsarinta baki ɗaya ta koma APC a jihar Kebbi yayin da dan takarar gwamna, yan takarar Sanata 3, da sauran yan takara a SDP duk sun rungumi APC. Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce yan siyasan sun yi abinda ya dace domin ci gaban Kebbi da jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel