Jam'iyyar SDP Ta Rushe Tsarinta, Ta Koma Inuwar APC Mai Mulki a Kebbi
- Ɗan takarar gwamna, masu neman sanata da majalisar wakilan tarayya na SDP sun sauya sheka zuwa APC a Kebbi
- Gwanna Atiku Bagudu, wanda ya tarbe su a sakatariyar kamfe da ke Birnin Kebbi, ya bayyana jin dadinsa
- Ya ce wannan matakin da suka ɗauka abu ne mai kyau da zai ɗaga Kebbi da jam'iyar APC
Kebbi - Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kebbi, Alhaji Atiku MaiAhu, ya jagoranci dukkan masu neman takara a SDP sun sauya sheka zuwa APC.
The Nation ta ce yan takarar Sanata da majalisar wakilan tarayya 34, da shugabannin SDP a gundumomi 225 da sauran jiga-jigai sun rushe tsari kana suka rungumi APC a Kebbi.
Yayin da yake maraba da masu sauya sheƙar a Sakatariyar kwamitin kamfen APC a Birnin Kebbi, gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ya nuna farin cikin da wannan ci gaba.
Bagudu, shugaban gwamnonin ci gaba na APC, ya yaba da matakin da masu sauya sheƙar suka ɗauka na sauya sheka zuwa All Progressive Congress mai mulki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Atiku Bagudu, yana da yakinin cewa masu sauya shekar sun ɗauki wannan matakin ne domin ci gaban jihar Kebbi da kuma jam'iyyar APC.
A jawabinsa ya ce:
"Har yanzun bamu kai yawa ba a jam'iyya domin adadin yawan mu shi ne ƙarfinmu kuma damarmu ta zaɓen yan takararmu sannan mu ci da jam'iyya da jiharmu zuwa gaba."
Bagudu ya taya shugaban APC na Kebbi, Alhaji Abubakar Muhammad, murna tarr da DG kwamitin kamfe, Alhaji Saidu Nasamu Dakingari, da sauran masu ruwa da tsakin da suka taka rawa wajen jan hankalin mutanen suka shiga APC.
Ɗan takarar gwamnan APC a jihar Kebbi, Dakta Nasir Gwandu, ya nuna farin cikinsa kana ya tabbatarwa 'yan siyasan cewa ba za'a nuna masu banbanci ba.
2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya
Dukkan yan takarar SDP da sshugabanni sun koma APC
A nasa jawabin, jagoran masu sauya shekar, Mai-Ahu, yace baki ɗaya yan takara da shugabannin SDP a sassan gundumomi 225 sun koma APC.
Sun News ta rahoto shi yana cewa:
"Muna da yan takara 12 masu neman majalisar jiha, 7 masu neman majalisar tarayya da uku da ke neman Sanata a shiyyoyi uku da ɗan takarar mataimakina, Alhaji Bello Tilli."
"Bayan haka mun rubuta wasikar janye wa daga SDP mun aika wa hukumar zaɓe ta kasa watau INEC."
Tawagar G5 bata mutu ba - Wike
A wani labarin kuma Gwamnan Ribas kuma jagoran G-5 ya ce za'a ga abinda zasu aikata a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023
A cewar gwamna Nyeson Wike duk yadda shugabannin PDP na ƙasa suka so sanin shirin G5 ba zasu sani ba amma a ranar zaɓen shugaban kasa zasu ga abinda zai faru.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da wasu ke ganin duk wani tururin tawagar gwamnonin ya lafa a yanzu kuma mai yuwuwa su yi wa Atiku aiki.
Asali: Legit.ng