Jam'iyyar APC A Kwara Ta Dakatar Da Sakatarenta, Ta Bayyana Dalili
- Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta Jihar Kwara ta dakatar da sakatarenta, Alhaji Mustapha Salman Isowo
- Sanarwar da aka fitar ta ce an dakatar da Isowo ne kan zarginsa da karkatar da kudaden yan jam'iyya da cin amanar jam'iyya
- A bangarensa, Alhaji Salman Isowo ya ce ya yi watsi da dakatarwar yana mai cewa 'karya' ake masa kuma hakan ba sabon abu bane a siyasa
Jihar Kwara - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kwara ta dakatar da sakataren ta, Alhaji Mustapha Salman Isowo, kan zargin yi wa jam'iyya zagon kasa da karkatar da kudade.
Mazabarsa ta Alanamu Central a karamar hukumar Ilorin ta Yamma ne ta dakatar da Isowo kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dakatarwar na cikin wani wasika ne da aka tura wa shugaban jam'iyyar, Prince Sunday Fagbemi, dauke da sa hannun shugabannin jam'iyyar 22, ciki har da ciyaman da sakatare, Alhaji Muyideen Ikolaba da Rafiu Onigbegi.
Wani sashi na wasikar ta ce:
"Sakataren jihar ya ki amincewa da shugabannin jam'iyyar da aka zaba bisa doka. Maimakon haka, ya kirkiro wasu shugabanni a mazabar don rushe ayyukan jam'iyyar kuma ya shirya tarurruka a wajen sakatariyar jam'iyyar a Isale Aluko.
"Sakataren jihar na jam'iyyar wanda yanzu aka dakatar da shi ya saba amfani da matsayinsa don karkatar da alawus din wata-wata da aka yi niyya ga unguwar da sauran kayan tallafi daga gwamnan da sauran yan takarar jam'iyyar ba tare da tuntubar zababben shugabannin mazabu da sauran mambobin jam'iyya ba."
Alhaji Isowo ya yi martani
A bangarensa, Alhaji Isowo ya yi watsi da zargin da aka masa yana mai cewa 'karya ne' kuma an saba yin hakan a siyasa.
Shugaban jam'iyyar na jiha, Prince Fagbemi, yayin magana da Daily Trust a kan lamarin, ya bayyana cewa matsala ce ta cikin gida kuma za a warware matsalar.
Gwamnan Legas ya dakatar da kamfen dinsa saboda karancin man fetur da sabbin naira
A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya dakatar da kamfen dinsa tare da rufe ofisoshinsa har sai baba ta gani.
Gwamnan ya dauki wannan matakin ne sakamakon wahalwahalun da al'umma ke ciki sakamakon karancin sabbin naira da man fetur a kasa.
Asali: Legit.ng