Tawagar G-5 Bata Mutu Ba, Zamu Taka Rawa Ranar 25 Ga Wata, Wike
- Gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa tawagar G-5 na nan da ranta ba ta rasa katabus ba kuma zasu ba da mamaki
- Nyesom Wike ya ce za'a ga matakin da gwamnonin zasu ɗauka ranar 25 ga watan Fabrairu zaɓen shugaban kasa
- Ya ce bai yi mamaki da jin labarin uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ta soke kamfen Ribas ba domin dama can ba su kaunar jihar
Rivers - Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya ce gwamnonin G-5 ko tawagar neman adalci da ta ɓalle daga inuwar PDP na nan da kuzarinsu kuma fafutukarsu ba ta mutu ba.
Channels tv ta tattaro gwamnan na cewa tawagar na nan zata fallasa ƙullin da ta yi ranar zaɓen shugaban ƙasa 25 ga watan Fabrairu. 2023.
Wike ya yi wannan jawabin ne a wurin ralin kamfen ɗan takarar gwamnan jihar wanda ya gudana a ƙaramar hukumar Ahoada ta gabas.
2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya
"Sun ce G-5 ta mutu, menene matsalarsu? Meyasa suka damu?" Gwamna Wike ya jefa tambaya yayin da yake jawabi ga dandazom magoya baya a wurin ralin ranar Talata."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Sun manta akwai lokacin magana kuma akwai lokacin ɗaukar mataki a siyasa. Zasu ga abinda zamu aikata ranar 25 ga watan Fabrairu, ba zasu taɓa sanin shirin mu ba ko sun matsa mana."
- Nyesom Wike.
Game da soke ralin ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a Ribas, gwamna Wike ya ce uwar jam'iyyar PDP ba ta kaunar mutanen Ribas tun farko.
"Lokacin da suka sanar sun soke Ralin ƙarya suke, ba su son fitowa su faɗa mana gaskiya cewa sun gaza tara mutane, duk da haka PDP ba ta taɓa gaya mana tana son Ribas ba."
"Mun sha fama da matsala a baya kamar Ambaliyar ruwa da ta mamaye gidajen mu. Kun ga wani ko ɗan takarar shugaban kasa ko wani shugaba ya zo jajanta mana?"
"Amma sun je Bayelsa da Delta, kun ga sun nuna a fili cewa ba su kaunarmu, kaddararmu a hannunmu take, ba wanda zai tilasta mana."
Aiwatar da Tsarin Sauya Fasalin Naira Siyasa Ce, Gwamna Wike
A wani labarin kuma Gwamna Wike ya soki sabon tsarin CBN na sauya fasalin takardun naira
Gwamnan, mamba a jam'iyyar PDP kuma jagoran G-5 ya ce tsarin CBN siyasa ce kuma masu goyon bayan aiwatar da shi ba su da tausayi.
A cewar Wike babu mai adawa da tsarin CBN ɗin amma yanayin yadda aka ɗauko aiwatar da shi ne akwai matsala duba da ganin yadda mutane ke wahala.
Asali: Legit.ng