Duk Da Goyon Bayan Buhari, Tinubu Ba Zai Kawo Katsina Ba, Tsohon Shugaban NHIS
- Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya yi hasashen cewa mutanen Katsina ba za su zabi Bola Tinubu ba a 2023
- Farfesa Yusuf ya ce Katsinawa sun gaji da mulkin APC don haka ba za su yi Tinubu ba duk da cewar Shugaba MuhammadunBuhari yana goyon bayansa
- Ya ce kan mutanen Katsina a waye yake don haka babu wani da zai zo ya nuna musu cewa su zabi wane kuma su bi shi
Katsina - Farfesa Usman Yusuf, tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), ya ce mutanen jihar Katsina ba za su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba a 2023.
Katsinawa sun gaji da gwamnatin APC da Buhari, Farfesa Yusuf
Da yake zantawa da gidan talbijin na Channels a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairu, Yusuf, wanda shine mai ba kwamitin kamfen dij Atiku/Okowa shawara kan tattaunawa da jama’a, ya ce mutanen Katsina sun gaji da gwamnatin APC.
Jaridar Daily Trust ta nakalto Yusuf yana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Siyasarmu a Katsina ta kasance mai karfi tun daga farko. Mu ba mutane bane da kowani mutum zai ce ka zabi wane. Idan Shugaba Buhari ya daga hannun sa a Katsina, ba Za mu zabe shi ba.
“Mutane sun gaji, sun kai bango. Sun kawo dandazon jama’ar da aka hayo daga Kano, mun ga motocin bas daga Kano. Ganduje ya lodo su daga chan. Yan siyasan nan na yin abubuwa da dama, don haka kada ka yarda da hangensu. Zahirin gaskiya a bayyane take.”
Jaridar The Cable ta rahoto cewa a yayin kamfen din APC a Katsina, da yake kira ga mutanen jihar kan su zabi Asiwaju Bola Tinubu, Shugaba Buhari ya daga hannun tsohon gwamnan na jihar Lagas don nuna lallai ya lamunce ma kudirinsa na son ya gaje shi.
Gwamnonin arewa ba za su iya kawo wa Tinubu jihohin ba, tsohon shugaban NHIS
A gefe guda, Farfesa Usman Yusuf ya ce babu wani gwamnan APC a arewa da zai iya kawo jiharsa ga Asiwaju Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewarsa duk basu da tasiri da farin jinin da za su iya hakan a wajen mutanensu.
Asali: Legit.ng