Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma a Jihar Imo
- Yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kutsa har ƙuryan cikin gida sun harbi shugaban PDP a gundumar Ogbaku, jihar Imo
- Rahotanni sun bayyana cewa ɗan siyasan ya shiga gida da misalin ƙarfe 9:00 na dare ba tare da sanin maharan sun yi wa gidansa tsinke ba
- Jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan jihar ya ce a yanzu sun fara bincike don kame masu hannu a harin
Imo - Wasu miyagun 'yan bindiga sun harbi shugaban Peoples Democratic Party (PDP) na gundumar Ogbaku, ƙaramar hukumar Mbaitolu ta jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa ɗan siyasan mai suna, Charles Oke, an harbe shi ne a gidansa da ke yankin Umunomo Nsokpo ranar Asabar da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi kwantan ɓauna a gidan shugaban PDP, wanda ya dawo gida ba tare da sanin tuggun da aka ƙulla masa ba da karfe 9:00 na dare.
Babbar Magana: Kwana 13 Gabanin Zabe, An Nemi Kuɗin Kamfen Atiku An Rasa, Jigon PDP Ya Tona Masu Hannu
Wasu majiyoyi daga yankin da abun ya faru sun ce 'yan bindigan sun harbi Mista Oke a ƙafafuwansa. Kum sun samu shiga gidan ta katanga.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar majiyoyin tuni aka garzaya da mutumin zuwa Asibitin da ba'a baygana ba domin kula da lafiyarsa.
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama's na jam'iyyar PDP a jihar Imo, Collins Opuruozor, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai da safiyar Litinin.
Mista Opuruozor, ya ce PDP na kan bincike kan abinda ya faru kuma ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba jam'iyya zata fitar da cikakken bayani game da harin.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen Imo, Henry Okoye, ya ce dakarun yan sanda sun fara binciken gano maharan da kuma damƙe su, kamar yadda Leadership ta rahoto.
"Mun kara tsananta sintiri a yankin da nufin dakile yunkurin sake kai sabon hari," inji Mista Okoye, mataimakin Sufuritandan yan sanda.
A wani labarin kuma 'Yan Daban PDP Sun Yi Garkuwa da Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Ribas
Rahotanni daga jihar sun nuna cewa an ji karar harbe-harben bingigu da yankin da lamarin ya faru, kuma wani ganau ya turo bidiyon halin da ake ciki.
Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da yan daba ke kai hari wuraren kamfe su ci karensu babu babbaka ba a jihar Ribas.
Asali: Legit.ng