Mun Nemi Kuɗin Kamfen Atiku Abubakar Mun Rasa a Imo Jigon PDP

Mun Nemi Kuɗin Kamfen Atiku Abubakar Mun Rasa a Imo Jigon PDP

  • Riginginun jam'iyyar PDP a jihar Imo sun bude sabon shafi yayin da ake zargin miliyoyin kuɗin kamfe sun sulale
  • Jigon jam'iyyar, Franklin Ngoforo, ya caccaki sakatare na ƙasa, Samuel Anyanwu da wadanda suke mara masa baya
  • PDP na fama da matsaloli da saɓanin cikin gida a tsakanin 'ya'yanta tun bayan gama zaben fidda yan takarar 2023

Imo - Wani jigon Peoples Democratic Party a jihar Imo, Franklin Ngoforo, ya yi zargin cewa sama da miliyan N60m daga cikin kuɗin kamfen ɗan takarar shugaban kasa da aka warewa jihar Imo sun ɓace.

Ngoforo ya faɗi haka ne yayin zantawa da 'yan jarida a Owerri lokacin da yake martani kan ƙorafin da aka shigar na neman rushe kwamitin gudanarwan PDP na jihar Imo.

PDP laima.
Mun Nemi Kuɗin Kamfen Atiku Abubakar Mun Rasa a Imo Jigon PDP Hoto: PDPNigeria
Asali: UGC

Babban jigon PDP ya kuma kalubalanci dukkan magoya bayan Sakataren jam'iyya na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Zabi Sabuwar Ranar Gudanar Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihohi Uku

A kalamansa, Mista Ngoforo ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Alal misali, ta ya jagororin jam'iyya kamar ofishin Sakatare na ƙasa zasu rika shiga gidajen Rediyo suna zagin jam'iyyarsu, suna rokon a rushe jam'iyyarsu, suna cin mutuncin mambobin kwamitin gudanarwa?"
"Ta ya makusantan Sakatare na ƙasa zasu yi sama da faɗi da sama da miliyan N60m da aka ware wa jihar Imo domin kaddamar da kamfen shugaban kasa kuma Ubangidansu yana basu kariya?"
"Kun taɓa ganin Sakataren PDP na kasa a wurin yawon kamfe ko rali ko wani zaman sauraron al'umna na jam'iyya? Ba shi kenan ba akwai saura."

Ya ƙara da cewa a bincike na karshe da suka gudanar sun gano cewa 'yan koren Anyanwu sun kai korafe-korafe sama da 10 gaban uwar jam'iyya ta ƙasa suna neman a tsige shugabannin PDP reshen Imo.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tsage Gaskiya, Ya Faɗi Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Iya Cin Zaben 2023

A cewarsa, kwana uku da suka gabata sun sake shigar da korafi kan shugabannin PDP na Imo, suna neman a rushe su baki ɗaya.

Tawagar Gwamnonin G-5 Ba Su Goyon Bayan Bola Tinubu, Jang

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Filato ya maida wa gwamna Simon Lalong martani kan tawagar gwamnonin G-5 na PDP

Jonah Jang ya karyata ikirarin Lalong wanda ya ce gwamnonin guda 5 sun amince zasu goyi bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262