Gwamna Matawalle Ya Ba Da Umarnin Damke Duk Wanda Baya Karban Tsohon Kudi

Gwamna Matawalle Ya Ba Da Umarnin Damke Duk Wanda Baya Karban Tsohon Kudi

  • Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ɗauki tsattsauran mataki kan masu ƙin karban takardun tsoffin kuɗi
  • Yayin rantsar da manyan alkalai, Matawalle ya umarci jami'an tsaro su kama duk wanda ya dena amsar tsohon naira a Zamfara
  • Ya kuma yaba wa matakin Kotun koli na dakatar da yunkurin CBN na haramta amfani da kuɗin daga ranar 10 ga wata

Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci a cafke duk wanda ba ya karɓan tsohon takardun N200, N500, N1000 a jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya ce tsoffin takardun naira guda uku da aka sauya suna da halascin amfani har zuwa lokacin da Kotun Koli zata yanke hukuncin ƙarshe kan Kes ɗin da jihohi uku suka kai FG da CBN.

Bello Matawalle.
Gwamna Matawalle Ya Ba Da Umarnin Damke Duk Wanda Baya Karban Tsohon Kudi Hoto: Bello Matawalle
Asali: Facebook

Matawalle ya bayyana haka ne a wurin bikin rantsar da manyan alƙalai da sabbin naɗe-naɗen hadimai wanda ya gudana a gidan gwamnatinsa, Chamber II a Gusau.

Kara karanta wannan

An Sami Mafita: Bayan Hukuncin Kotu, Yan Najeriya Sun Bukaci CBN Ya Musu Abu 1 Tak Kan Sabbi da Tsoffin Kuɗi

Ya kara da cewa shi da takwarorinsa na jihohin Kaduna da Kogi sun garzaya Kotun Koli domin ta umarci a tsawaita wa'adin amfani da tsoffin takardun N200, N500, da N1000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamnasa, gwamna Matawalle ya ce:

"Kamar yadda kuka sani, tattalin arzikin ƙasar nan ya shiga halin kakanikayi sanadin yunkurin babban banki na haramta hada-hada da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 daga 10 ga watan Fabrairu."
"Wannan ya ƙara hargitsa jiharmu wacce tuni take fama da matsaloli kamar na 'yan fashin daji da wasu muggan laifuka da suka kawo tabarbarewar tattalin arziki a jihar nan da maƙotanta."
"Bisa la'akari da haka da wahalhalin da mutane suka shiga, muka yanke haɗa kai da jihohin Kogi da Kaduna muka tafi Kotun Ƙoli domin tabbatar da tsoffi da sabbin kuɗin sun ci gaba da amfani har bayan 10 ga watan Fabrairu."

Kara karanta wannan

Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

Rahoton Punch yace gwamna Matawalle ya yaba da matakin da Kotun Koli ta ɗauka na dakatar da yunkurin CBN, wanda a cewarsa ya rage wa mutane wahalhalun da suka shiga.

Buhari ya kebe da Bola Tinubu a Abuja

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na APC a Villa

Rahotanni sun bayyana cewa jagororin jam'iyya mai mulkin sun shiga ganawar ne da misalin karfe 9:45 na daren Jumu'a 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Wata majiya ta ce duka da ba'a faɗi abinda zasu tattuna ba amma zaman ba zai rasa alaƙa da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓe ba nan da mako biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262