Zaben 2023: APC Ta Dage Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Kano

Zaben 2023: APC Ta Dage Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Kano

  • Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a Najeriya ta dage taron yakin neman zaben ta na shugaban kasa da aka shirya yi a Kano
  • Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na APC, Festus Keyamo, SAN, ya tabbatar da hakan
  • Keyamo ya ce dagewar ba wani abu bane illa irin sauye-sauye da aka saba yi yau da kullum kuma ya ce ba a tsayar da sabuwar rana ba

Jihar Kano - A yayin da ake tunkarar babban zabe a watan nan, kwamitin yakin neman zabe na shugaban kasa ta Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta dakatar da kamfen dinta a Kano har sai baba ta gani.

Da farko an shirya yin taron yakin neman zaben ne a ranar 16 ga watan Fabrairun shekarar 2023, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Mai Goyon Bayan Atiku, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi, Ya Yaba Wa Bola Tinubu

APC Rally
APC Ta Dage Taron Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Festus Keyamo, SAN, direktan watsa labarai na kwamitin kamfen din na takarar shugaban kasa na APC, ya tabbatar wa Daily Trust hakan a ranar Juma'a cewa an dage kamfen din.

A cikin wani sakon WhatsApp, Keyamo ya ce:

"Eh, ba a zabi sabuwar rana ba."

Da aka tambaye shi ya fadi dalilin dage taron, Keyamo ya bada amsa da cewa:

"gyare-gyare ne da ake yi na yau da kullum."

An shirya gangamin ne a matsayin wani bangare na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima gabanin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kwankwaso: Babu wani dan Najeriya da zai zabi APC da PDP idan yana cikin hankalinsa

A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya ce babu wani dan Najeriya wanda zai zabi PDP ko APC idan yana cikin hankalinsa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Goyi Bayan Tinubu? Gwamnan Ribas Ya Amince Dan Takarar APC Ya Yi Taro Kyauta A Filin Wasa

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya furta hakan ne a ranar Litinin lokacin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi a wurin kamfe din dan takarar gwamna na NNPP da aka yi a karamar hukumar Tarauni a Kano.

Kwankwaso ya cigaba da cewa jam'iyyun na PDP da APC ba su kaunar matasa da matan Najeriya, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel