Jam'iyyun Adawa 29 Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu da Gwamnan Legas
- Kwanaki 16 gabanin babban zaben shugaban kasa, jam'iyyun siyasa 29 masu adawa sun yanke marawa Tinubu baya
- Jam'iyyun sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na APC ya yi an gani a jihar Legas
- Haka zalika ƙungiyar gamayyar jam'iyyun ta ayyana goyon bayan kudirin tazarcen gwamna Sanwo-Olu
Lagos - Jam'iyyun adawa 29 a jihar Legas sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC da gwamna Babajide Sanwo-Olu, mai neman tazarce.
Shugaban gamayyar jam'iyyun siyasa reshen Legas (COPPILS), Akinola Obadia, ne ya tabbatar da haka ga manema labarai, kamar yadda rahoton The Nation ya tattaro.
Ya ce sun ɗauki Bola Tinubu duba da dumbin nasarori da ci gaban da ya assasa lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Legas.
A jawabinsa ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bisa la'akari da nasarorinsa, daga yau muna goyon bayan Tinubu a matsayin wanda ya dace da aikin, ya mulki Najeriya kuma ya tsamo ta daga ƙaƙanikayi idan ya zama shugaban kasa."
Haka zalika gamayyar jam'iyyun adawan sun sha alwashin harhaɗa wa ɗan takarar shugaban kasan da gwamnan APC kuri'u miliyan biyu.
Wane jam'iyyu ne suka ɗauki wannan matakin?
Legit.ng Haua ta fahimci cewa jam'iyyun sun haɗa da AD, UPN, UPP, NPC, ACPN, CPN, BNPP, PPP, PPA, NUP, UP, LM, Mega Party, MMN, FJP, NCMP, GDPN, da APA.
Sauran kuma su ne, AGAP, ID Party, RPN, Green Party, Hope Democrats, DA, C4C Party, NPM, kda kuma ta ƙarshe jam'iyyar Independent Democrats.
A ruwayar Leadership, Obadia ya ci gaba da cewa:
"Mun amince baki ɗaya cewa mu koma wurin dumbin magoya bayanmu wadanda ba mambobin APC bane mu gaya masu dalilin da yasa Tinubu ya fi dacewa da ƙasa."
"Mu gaya masu Babajide Sanwo-Olu ya cancanci a ba shi dama ta biyu domin ya kammala ayyukan Alherin da ya ɗauko a jihar Legas."
Dalilin Da Yasa Peter Obi Zai Samu Kuri'u da Yawa a Arewa a Zaben 2023
A wani labarin kuma Jigo LP ya bayyana babban dalilin da zai ingiza yan arewa su zabi Peter Obi a zabe mai zuwa
Ibrahim Abdulkarin, daraktan kwamitin kamfen Obi mai zaman kansa ya ce mutane a arewa sun fusata sakamakon halin da suka shiga.
Mista Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party na ɗaya daga cikin masu neman gaje Buhari na sahun gaba.
Asali: Legit.ng