Jam’iyyar APC ta Fitar da Matsaya a Kan Daga Zaben Shugaban kasa da ‘Yan Majalisa
- Felix Morka ya ce Jam’iyyar APC ba ta neman a fasa yin zabe, yake cewa sun shirya da kyau
- Sakataren yada labaran APC ya ce rade-radin cewa su na goyon bayan a daga zabe, karya ce
- Jam’iyyar tana sa ran mafi yawan ‘Yan Najeriya za su zabi Bola Tinubu da sauran ‘yan takaransu
Abuja - Jam’iyyar APC mai shugabanci a Najeriya ta karyata rade-radin da ake yi na cewa tana neman a dakatar da zaben shugaban kasa da na majalisa.
Premium Times ta fitar da rahoto cewa jam’iyyar APC ta fitar da matsayarta ne a wani jawabi daga bakin sakatarenta na yada labarai, Mr. Felix Morka.
A jawabin da Morka ya fitar a ranar Laraba, ya ce maganar goyon bayan daga zabe, ba gaskiya ba ne.
Kakakin na APC na Najeriya yake cewa sun samu jita-jita na yawo a kan neman a fasa yin zaben shugabannin kasa a ranar da hukumar INEC ta tsaida.
Buhari yana goyon bayan ayi gaskiya
A matsayinsa na sakataren yada labarai na jam’iyya, Morka ya ce APC da Mai girma shugaba Muhammadu Buhari su na goyon bayan ayi zabe na gaskiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton ya ce jam’iyyar APC ta ce tun farko an fito da labarin ne saboda a yaudari al’umma kurum.
Jawabin Felix Morka
“Hankalinmu ya je ga rahoton bogi da ke yawo a wasu gidajen yada labarai cewa jam’iyyar APC tana kokarin ganin an daga babban zabe na 2023.
Karara wannan rahoto karya ne, babu kanshin gaskiya a ciki. A labarin, babu bayani mai tsoka mai gaskata zargin, hakan ya nuna yaudara aka manufa.”
Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC
Sha’anin zabe ya shafi harkar tsaro da zaman lafiyar kasa. Bai dace a bar wannan lamari ga ganganci, rashin tunani da gaggawar ‘yan jarida ba.
Abin da yake gaskiya shi ne a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari, jam’iyyarmu ta yi kamfen da ya fi kowane a tarihi domin a zabi Bola Tinubu.
- Felix Morka
Najeriya sai Tinubu/Shettima
Morka yake cewa sun tsaya tsayin daka wajen ganin Tinubu, Kashim Shettima da sauran ‘yan takaran majalisa da na jihohi sun yi galaba a zaben bana.
The Cable ta ce yunkurin canjin wasu takardun kudi da bankin CBN ya yi ne ya jawo ake irin wannan rade-radi, duk da INEC ta ce ba za a fasa zabe ba.
Mun shiryawa babban zabe, kuma mu na sa ran dinbin ‘Yan Najeriya za su sake kada mana kuri’a a zaben kwarai wanda yake cikin zaman lafiya.
- Felix Morka
Bayanin samun N280m a banki
A baya kun samu rahoto cewa magana ta fara fitowa game da zargin ICPC na samun sama da Naira miliyan 280 a wani bankin 'yan kasuwa a Abuja.
A lokacin da jami’an ICPC suka kawo samame a Abuja, bankin sun ce ana raba sababbin kudi a na’urorin ATM kamar yadda CBN ya yi umarni.
Asali: Legit.ng