Obasanjo Yayi Bayani kan Zargin Yadda Ake Kokarin Hana Yin Zaben 2023
- Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce yana fatan a yi zaben 2023 mai zuwa kada a daga shi saboda dalilai
- Obasanjo yace duk kasashen duniya Najeriya ta ke kallo kuma sun san halin da ake ciki don haka yana fatan kada a daga zabukan
- Ya bayyana yadda ya ziyarci kasashe uku da Afrika kuma dukkansu sun ce suna zuba ido ne a kammala zabukan Najeriya
Abeoukuta, Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana fatansa na cewa kada wani abu ya zo ya hana zaben watan Fabrairu da Maris masu zuwa.
Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan zabukan yayin da mambobin kwamitin yardadda na jam'iyyar ADC suka ziyarcesa a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Tsohon shugaban kasan ya sanar da hakan ne sakamakon halin da 'yan kasar nan ke cikin saboda rashin takardun sabbin kudi da man fetur wanda ka iya sa dole a dage zaben, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamitin yardaddun ya samu jagorancin shugaban, Mani Ahmed, shugaban jam'iyyar na kasa, Ralph Nwosu da tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Chukwuka Monye.
Obasanjo yace:
"Muna cikin wani hali a Najeriya, kasa da makonni uku za a yi zabe. Toh ina fatan babu abinda zai hana hakan. A kasa da makonni uku, za mu zabi shugaban da zai karba ragamar Najeriya na tsawon shekaru hudu.
"Dukkanmu da ke Najeriya, kamar yadda na fadi da safen nan, na je Togo, Ghana da Cote d'Ivoire daga farko makon nan kuma sun damu da abinda ke faruwa a Najeriya."
Obasanjo yace dole ne 'yan Najeriya su yi duk abinda ya dace don ganin an yi zaben kamar yadda aka tsara.
Ya kara da cewa, duniya ta matukar mayar da hankali wurin ganin cewa Najeriya tayi zabenta lokacin da ta tsara, jaridar Premium Times ta rahoto.
"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira
Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan Machina da Lawan
A wani labari na daban, kotun koli ta ce Ahmad Lawan ne halastaccen 'dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa a jam'iyyar APC.
Kotun ta fatattaki Bashir Machina, wanda yayi nasarar shari'ar a kotun tarayya har zuwa ta daukaka kara da aka yi.
Asali: Legit.ng