Karancin Mai Da Sabbin Naira Ba Zai Hana Yin Zaben 2023 Ba, Shugaban INEC Ya Tabbatarwa 'Yan Najeriya
- Duk da halin da yan Najeriya ke ciki na karancin man fetur da Naira, shugaban INEC ya ce za a yi zabe
- Farfesa Yakubu Mahmood ya ce karancin Fetur da Naira ba zai hana zabe a ranar 25 ga watan Fabrairu ba
- Mahmood ya ce an shawo kan kalubalen da hukumar ta hango tun farko tattare da sabon manufar CBN kan kudi
Abuja - Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa za a gudanar da babban zaben kasar mai zuwa kamar yadda aka tsara.
Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, yayin wata ganawa da majalisar zartarwa ta kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar The Cable ta rahoto.
An shawo kan kalubalen hukumar INEC, Mahmood
Jawabin shugaban INEC din na zuwa ne a daidai lokacin da yan Najeriya a fadin kasar ke fama da matsin rayuwa dakamakon karancin man fetur da na sabbin takardun naira.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ana dai ta nuna damuwa game da yadda halin da ake ciki zai iya shafar gudanarwar babban zaben shugaban kasa da na gwamna da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma 11 ga watan Maris.
Mahmood ya bayyana cewa hukumar ta magance kalubalen da ta hango tun farko tattare da karancin na man fetur da kudin, jaridar The Nation ta rahoto.
Shugaban INEC ya gana da Gwamnan CBN
Idan za ku tuna, mun kawo a baya cewa shugaban hukumar zaben ta kasa ya yi wata ganawa da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, don tattauna kalubalen da INEC ke fuskanta a kan sabon manufar babban bankin.
Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a
Mahmood ya sanar da Emefiele cewa akwai abubuwan da dole idan hukumar zaben za ta aiwatar dangane da shirye-shiryen zaben na 2023 za ta bukaci tsabar kudi wanda ake fuskantar rashin wadatuwarsu a kasar yanzu haka.
Sai dai kuma, Emefiele ya ba INEC tabbacin cewa zai ba ta dukkanin goyon bayan da take bukata wajen gudanar da zabe cikin nasara ba tare da tangarda ba. Ya kuma ce CBN zai samar da duk kudaden da suke bukata don harkokinsu na zabe.
Asali: Legit.ng