Hotuna: Tinubu ya Ziyarci Hajiya Dada, Mahaifiyar Marigayi Yar’adua, a Katsina
- Bola Tinubu, Jagaban Borgu kuma mai rike da tutar jam’iyyar APC don takarar shugaban kasa, ya ziyarci Hajiya Dada a Katsina
- Tinubu ya je gangamin yakin neman zabensa ne a jihar Katsina yayin da ya kai wa mahaifiyar marigayi Shugaba Yar’adua ziyara har gida
- A Hotuna da suka fita, Tinubu ya zauna tare da Hajiya Dada har cikin dakinta inda wasu daga cikin iyalanta suka dinga daukarsu hotuna
Katsina - Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, ya kai wa mahaifiyar marigayin tsohon shugaban kasan Najeriya, Umaru Musa Yar’adua, ziyara a garin Katsina.
Ya ziyarci tsohuwar ne yayin da je jihar gangamin yakin neman zabensa, Aminiya ta rahoto.
A Hotunan da suka bayyana, na ga Tinubu da Hajiya Dada tare da wasu daga cikin iyalanta da masu rakiyar Tinubu ana ta daukar hoto.
Cike da annashuwa da farin ciki ‘dan siyasan ya zauna kusa da tsohuwar ana daukar su hoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ga wasu daga cikin hotunan:
Ba wannan karon bane na farko da fitattun ‘yan siyasa ke Kaiwa mahaifiyar tsohon shugaban kasan ziyara matukar suka dira a Katsina.
Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya ziyarci HaJiya Dada yayin da ya je jihar Katsina.
Tinubu ya Gwangwaje wadanda harin ‘yan bindiga ya ritsa dasu a Katsina da kyautar N100 miliyan
A wani labari na daban, Bola Ahmed Tinubu, ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ba wa iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya ritsa da su a Katsina baya-bayan nan.
Miyagun ‘yan bindiga dai sun halaka ‘yan sa kai a kalla 80 a mummunan farmakin da suka kai a cikin makon da ya gabata.
Mummunan al’amarin nan mai tada hankali ya faru ne a karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina.
Hotunan gawawwakin jama’a da aka halaka din sun bayyana wanda hakan ya tada hankulan al’umma.
An ga yadda aka jere su reras aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin Islama ya tanadar yayin da jama’a daga sassan kasar nan suka dinga mika ta’aziyyarsu tare da nan hakuri ga iyalansu.
Asali: Legit.ng