Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Da Gwamnan CBN Sun Sa Labule Ana Tsaka Da Karancin Naira

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Da Gwamnan CBN Sun Sa Labule Ana Tsaka Da Karancin Naira

  • Gwamnan babban bankin CBN da shugaban hukumar zabe sun yi wata ganawa mai muhimmanci yan kwanaki kafin zabe
  • Farfesa Mahmood Yakubu da Godwin Emefiele sun tattauna kalubalen da hukumar INEC ke fuskanta wajen samun sabbin kudi da za ta aiwatar da harkokin zabe
  • Ana fama da matsalar karancin takardun Naira a Najeriya yayin da wa'adin CBN na daina amfani da tsoffin kudi ke kara gabatowa

Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wata ganawa da Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Yakubu ya samu rakiyar kwamishinonin zabe na kasa 11 zuwa wajen taron da aka yi a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu, Channels TV ta rahoto.

Shugaban INEC da Gwamnan CBN
Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Da Gwamnan CBN Sun Sa Labule Ana Tsaka Da Karancin Naira Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

A jawabinsa, shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa sun yi ganawar ne saboda babban bankin kasar na da muhimmiyar rawar ganin da za ta taka wajen gudanar da zabe.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

Sai dai kuma, musamman wannan taron ya karkata kan manufar cire kudi da CBN ya zo da shi a baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Nuwamban 2022 ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 yana mai jaddada shirin CBN na kawo karshen tsoffin kudin a ranar 31 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma, an dage wa'adin daina amfani da tsoffin kudin har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

Dalilin ganawar shugaban INEC da Gwamnan CBN

Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar na fuskantar kalubale da wannan manufar kasancewar akwai ayyuka da dama da hukumar za ta aiwatar da tsabar kudi.

A cewarsa, yawancin kayan zabe da za a yi aiki da su a zaben da tsabar kudi za a siye su.

Yakubu ya kara da cewar ya halarci zaman ne don tattaunawa da gwamnan na CBN game da yadda za a magance lamarin.

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

A martaninsa, Emefiele ya jaddada goyon bayan da CBN ke baiwa INEC, yana mai cewar zai ci gaba da aikata hakan.

Ya ba hukumar tabbacin cewa saboda irin matsayin da aka ba CBN a zaben, babban bankin zai gabatar da duk abun bukata ga INEC don ta biya harkokinta.

Emefiele ya kuma bayyana cewa babban bankin ba zai yarda ayi amfani da shi wajen kawo tangarda a zabe mai zuwa ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Ga hotunan ganawar a kasa:

Gwamnan CBN na son kawo rudani a zaben 2023, Ganduje

A wani labarin, gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya zargi gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da kokarin kawo rudani a babban zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng