Karancin Naira: Wike Ya Aike Wa Buhari Sako A Fakaice, Ya Ce, "Ina Son Ka Gama Lafiya", Kalli Bidiyon
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi kira da a dakatar da sabon tsarin sauya fasalin na Naira, wanda ya ke kallo a matsayin illa ga al’umma
- Wike ya bayyana cewa fatarsa ga shugaban kasar shine ya gama lafiya amma wannan tsarin ba masalaha bane ga al'umma kuma ba zai kawo karshen rashawa ko siyar da kuri'a ba yayin zabe
- A cewar Wike, ba zai yi wu mutane suna da kudade a asusunsu na banki ba amma ba za su iya amfani da kudin ba
Fatakwal, Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a Najeriya ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da sabon tsarin sauya fasalin takardar kudi na Naira, wanda yake ganin yana da illa ga al'umma.
Gwamnan wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP, ya amince da kyawawan aniyar shugaban kasar na farfado da tattalin arziki, yaki da cin hanci da rashawa, da kuma daina sayen kuri’u.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai ya yi imanin cewa karancin kudin Naira na azabtar da jama’a kuma sabuwar manufar ba za ta warkar musu da matsala ba.
Abin da Wike ya fada wa Shugaba Buhari kan karancin naira
Wike ya ce tsarin ba zai yi maganin rashawa ba kamar yadda ake tsammani kuma ba zai hana siyan kuri'u ba kamar yadda shugaban kasar ke tunani, sai dai kara azabtar da talakawa.
Ya ce ba daidai bane mutane suna da kudi a bankuna amma ba za su iya amfani da kudin ba, yana mai cewa hakan zai iya bata wa shugaban kasar suna.
Gwamnan ya ce:
"Shugaban kasa, ina son ka gama lafiya amma wannan tsarin sauya fasalin nairan ba alheri bane ga al'umma, talakawa ne ke shan wahala ba yan siyasa ba."
Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi
Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da Wike, Shugaba Muhammadu Buhari, sauya fasalin naira, karancin naira, zaben 2023
Gwamnan ya ce ya fahimci matsin lamban da ke kan shugaban kasar na farfado da tattalin arziki, yaki da rashawa da hana sayar da kuri'u amma ya ce wannan tsarin ba zai haifar da komai ba sai karin matsala ga al'umma.
Kalaman gwamnan na zuwa ne awanni bayan Shugaban kasar ya yi kira ga yan Najeriya su bashi kwana 7 don ya magance matsalar da suka taso sakamakon sauyin sabon takardar nairan.
Ga bidiyon a kasa:
2023: Jam'iyyun siyasa 10 sun mara wa Atiku baya a jihar Anambra
A wani rahoton, Farfesa Obioro Okonkwo, babban direktan yakin neman zaben Atiku/Okowa ya ce a kalla jam'iyyun siyasa 10 ne suka marawa Atiku Abubakar baya gabanin zaben shugaban kasa na 2023 a Anambra.
Asali: Legit.ng