El-Rufai: Karamar Hukumar Daya A Kaduna Za Ta Shafe Kuri'un Anambra Da Peter Obi
- Gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufai ya bayyana cewa Peter Obi bashi da yadda za ayi yaci zabe a Najeriya
- El-Rufai ya bayyana cewa ko da Peter Obi zai lashe Anambra da kaso 70, wanda ya lashe Kano da kaso 10 ya fishi
- El-Rufai ya kuma shaida cewa kuri'un karamar hukuma daya a Jihar Kaduna zai shafe yawan kuri'un Anambra gaba daya
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce karamar hukuma daya a Kaduna za ta shafe gaba daya kuri'un da dan takarar jam'iyyar LP Peter Obi zai samu a Anambra, rahoton Daily Trust.
Obi, wanda ya yi gwamnan Anambra sau biyu, yana ikirarin cinye Anambra gaba daya wanda daga jihar ya fito, a zabe mai zuwa.

Asali: Facebook
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma da yake hira da gidan talabijin na TVC, El-Rufai ya kore yiwuwar cin zaben dan takarar jam'iyyar LP, ya ce bazai je ko ina a zaben ba.
Ya bayyana Obi a matsayin jarumin wasan Nollywood, tare da fadin, ''iya haka zai tsaya''.
Ya ce:
''Peter Obi ya lashe zabe? Peter Obi yana da kaso daya a Sokoto, kaso biyu a Katsina, kaso biyar a Kano, haka kuri'un suke, jihohin ba kan su daya ba.
''Don kana da kaso 70 a Anambra ba yana nufin in mutum ya samu kaso 10 a Kano bai fika ba.
''Mutum miliyan 4 ne takaimaiman masu kada kuri'a a Kano, Anambra fa, kuri'un Anambra basu fi karamar hukuma daya a Jihar Kaduna ba.
''Don haka ba duk jihohin ne daya ba, eh Peter Obi zai mamayi Kudu, zai iya kawo Kudu maso kudu, sai kuma ina?."
Ya cigaba da cewa:
''Bashi da yawan kuri'u a kudu maso yamma sai dan digo kadan daga Lagos, zai samu kuri'un kiriatocin arewa, zai samu da yawa amma nawa suke? Nawa ne?
''Peter Obi ba zai iya cin zabe ba, bashi da adadi a jihohi, bashi da kaso 25 a fiye da jihohi 16, ba zai kai labari ba. Peter Obi dan wasan kwaikwayo ne kuma iya abin da zai tsaya kenan.
''Wannan zabe ne tsakanin PDP da APC saboda suke da tasiri, sun watsu ko ina. Kabilanci da ci da addini ba zasu kaika ko ina ba kuma haka jam'iyyar LP take yi.''
2023: Gwamna El-Rufai ya yi karin haske kan manyan da ya ce suna yi wa Tinubu zagon kasa
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce zai fallasa wasu daga cikin manyan mutanen da ke yi wa Bola Tinubu zagon kasa gabanin zaben 2023.
El-Rufai, cikin wata hira da kafar BBC Hausa ta yi da shi ya yi karin bayani kan wadanda ya ke zargin da adawa da takarar Tinubu.
Asali: Legit.ng