Aisha Buhari Ta Goyi Bayan El-Rufai Na Cewa Wasu Na Kusa Da Mijinta Basu So Tinubu Yaci Zabe

Aisha Buhari Ta Goyi Bayan El-Rufai Na Cewa Wasu Na Kusa Da Mijinta Basu So Tinubu Yaci Zabe

  • Akwai kamshin gaskiya a rade-radin da ake yi game da kulla-kullan da wasu ke yi kan Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC
  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai wasu na kusa da fadar shugaban kasa da ke shiryawa Tinubu manakisa
  • Don nuna goyon bayanta ga batun, matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta daura bidiyon El-Rufai a shafinta na soshiyal midiya

Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta goyi bayan bidiyon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya zargi wasu a fadar shugaban kasa da rashin son dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ci zabe.

El-Rufai ya ce wadannan mutanen na fadar shugaban kasar sune wadanda yan takarar da suke so suka sha kaye a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar kuma har yanzu abun na yi masu ciwo.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

El-Rufai, Aisha Buhari da Tinubu
Aisha Buhari Ta Goyi Bayan El-Rufai Na Cewa Wasu Na Kusa Da Mijinta Basu So Tinubu Yaci Zabe Hoto: Nasir El-Rufia, Aisha Buhari, Bola Tinubu
Asali: Facebook

Aisha ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, yan awanni bayan El-Rufai ya yi magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV.

Matar shugaban kasar wacce ita ke jagorantar jirgin yakin neman zaben Tinubu ta yi wa wallafar tata take da:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

#longlivethefederalrepublicofnigeria” wato Allahyajadarantarayyarnajeriya.”

Gwamnan na jihar Kaduna dai ya ce wadannan mutane da bai bayyana sunansu ba suna fakewa a bayan Shugaba Buhari suna kokarin cimma kudirinsu na ganin Tinubu ya fadi zabe.

Fadar shugaban kasa ta yi martani ga El-Rufai

A halin da ake ciki, fadar shugfaban kasa ta yi martani ga ikirarin gwamnan jihar Kaduna na cewa ana yi wa takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'ioyyar APC zagon kasa.

Da yake martani, ministan labarai, Lai Muhammad ya sake nanata matsayin shugaban kasa na mayar da hankali wajen tabbatar da ganin an yi zabe na gaskiya.

Kara karanta wannan

Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa

Ja kuma bayyana cewa su dai basu da masaniya kan wadanda ke yi wa dan takarar na APC zagon kasa a cikin fadar gwamnatin.

A wani labarin, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin Najeriya a 2023 abun dariya ne domin dai aikin shugabancin kasa ba na yan shekaru 40 zuwa 50 bane..

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng