2023: Ya Zama Wajibi Mu Guji Zagin Mutane, Sarkin Musulmi Ya Gargadi Atiku
- Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargaɗi 'yan siyasan kasar nan su guji zage-zage da aibata juna
- Mai Alfarma Sarkin ya yi wannan gargaɗi ne yayin da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugagan kasa ya kai masa ziyara fada
- Shugaba a Addinin Musulunci ya ce ya zama wajibi mutane su guji ayyukan da zasu gurbata masu rayuwarsu ta lahira
Sokoto - Yayin da harkokin kamfe suka kankama gabanin zaɓe, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargaɗi 'yan siyasa su guji hantara da zagin juna.
Sarkin Musulmi ya yi wannan gargaɗin ne ranar Talata sa'ilin da ya karbi bakuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, a fadarsa dake Sakkwato.
Channels tv ta tattaro cewa yayin da Atiku ya kai masa ziyara, Sarkin Musulmi ya ce:
"Duk abinda zaka yi ka ji tsoron Allah, idan ka yi imani Allah ke bayarwa kuma ya hana to zaka samu nasara kuma zaka yi kyakkwan karshe. Wannan rayuwar kalilan ce dole mu yi aiki domin rayuwar lahira."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya zama tilas mu guji zagin mutane, mu guji aibata mutane, kar mu raba alaƙa da abokantaka a kowace jam'iyyar siyasa muke. Abu mai muhimmanci shi ne Allah ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so."
"Kuma Allah ne ke kwace mulki daga wanda ya ba a lokacin da ya so ba tare da ya ba shi Notis ba."
Shugaban Addinin ya kuma bayyana cewa ya zama tilas ga 'yan Najeriya daga kowane yanki su yi aiki da haɗin kai, gaskiya da yarda da juna.
"Mun yi imani da cewa idan muka yi haka cikin gaskiya da gaskata juna, muka sa tsoron Allah SWT a zukatanu, ina da yakinin wannan ne ainihin tushen abinda muke bukata."
Thisday ta tattaro cewa Atiku da tawagar yakin neman zaɓensa sun je Sakkwato ne a ci gaba da yawon tallata zaɓen PDP a watan Fabrairu.
Turmutsitsi a wurin kamfe ya yi ajalin hadimar gwamna a Sokoto
A wani labarin kuma Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto
Babbar mai ba gwamna Aminu Tambuwaƙ shawara kan harkokin ilimin mata, Hajiya Aisha Maina, ta rasa ranta yayin da turereniya da cunkoso ya rutsa da ita a wurin kamfe.
An tattaro cewa Hajiya Maina ta shiga cikin wani cinkoso da hargitsi da ya uku a hanyar fita daga cikin filin kwallon Giginya, wurin da Atiku ya gudanar da Rali.
Asali: Legit.ng