Abinda Marigayi Sarkin Dutse ya Sanar da Buhari Makon da ya Gabata da ya ZIyarcesa

Abinda Marigayi Sarkin Dutse ya Sanar da Buhari Makon da ya Gabata da ya ZIyarcesa

  • Mai martaba marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, sarkin Dutse na jihar Jigawa ya karba bakuncin Tinubu a fadarsa ranar 22 ga watan Janairu, 2023
  • Marigayin basaraken ya bayyana yadda suke da kamanceceniya, a gogewar rayuwa, ilimi, hada kan al'umma da sauransu iri daya da Bola Tinubu
  • Bayan nuna goyon bayansa dari bisa dari ga Tinubu, ya yi wasu kalamai da suka yi kama da wasiyya, wanda Tinubu ya yi alkawarin cikawa a gaban wasu kososhin APC da suka yi masa rakiya fadar

Dutse, Jigawa - Mai martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, Sarkin Dutse na jihar Jigawa, ya karbi 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadarsa ranar 23 ga watan Janairu, 2023.

Marigayin basarake
Abinda Marigayi Sarkin Dutse ya Sanar da Buhari Makon da ya Gabata da ya ZIyarcesa. Hoto daga BBC Hausa News
Asali: Facebook

A kalla gwamnoni shida na APC, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar tarayya ne suka rako Tinubu, wanda ke fatukar niman kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Halin da Ake Ciki Tsakanin Tinubu da Shugaban Kasa – Sanatan APC Ya Fayyace Komai

Yayin tarbar 'dan takarar shugaban kasar, marigayin basaraken ya ce akwai abubuwan da suke da kamanceceniya da 'dan takarar, Daily Trust ta rahoto.

Sarkin ya ce ko tantama baya yi cewa Tinubu zai iya jagorantar kasar kamar yadda ya kwatanta a tarihin ayyukan da ya yi lokacin yana gwamnan Legas da sauran ayyukan da ya yi na siyasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Ina daya daga cikin mabiyanka da irin ayyukan siyasarka. Kai ne mutum daya da na yi amanna zai iya ko yana da kwazon mulkar kasa. A da Najeriya yanki biyu ce. Ka yi nasarar hada kan Arewa da yamma karkashin wannan mulkin.
"Na halarci bikin rantsarwarka a matsayin Jagaban na Borgu da marigayi Sarkin Borgu ya nada ka. Aboki na ne. Yana maganarka da kyawawan halayenka.
"Kai ma ka tafi Amurka don kayi karatu kamar ni. Kuma kamar kai, ni ma nayi buga-buga da dama don in rayu.

Kara karanta wannan

Laifin APC Da Ganduje Ne Harin Da Aka Kaiwa Buhari a Kano, PDP Ta Tona Asiri

"Nima akawu ne kamar ka. Na karanta wasu daga cikin littafanka musamman mai taken 'Financialism'. Kawai abun da ya bambantani da kai, shi ne siyasa da bana yi."

Sarkin ya ce duk da ya saba tarbar baki a fadarsa ba a masauki ba, amma ya bambanta ga gwamna jihar, Badaru Abubakar, a matsayin girmamawa ga Tinubu, ya yanke shawarar tarbarsa a masaukinsa.

Sai dai, Sarkin ya tunatar da 'dan takarar APC cewa babu ruwa a Jigawa, inda ya bukace shi da ya yi aiki tare da jihar don kawo karshen matsalar ruwa, da sauran abubuwa idan ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa.

Tinubu ya ce ya yanke shawarar kai ziyarar ban girma ga Sarkin a matsayinsa na "shugaba kuma uba" don neman goyon bayansa a tafiyarsa ta shugabancin kasa.

Ya ba basaraken da sauran wadanda ke wurin tabbacin zai yi aiki tukuru don magance matsalolin da ke addabar kasa, inda ya kara da cewa:

"Ba zai siyar ko raba arzikin kasa kamar alawa ba. Ya zo ne don aiki kuma zai ma kasa aiki."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng