Babban Jigon Jam'iyyar APC A Jihar Ondo Ya Sauya Sheka Zuwa LP

Babban Jigon Jam'iyyar APC A Jihar Ondo Ya Sauya Sheka Zuwa LP

  • Jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Ondo ƙasa da kwana 30 gabanin babban zaben 2023
  • Honorabul Stephem Adeyeri, ya tabbatar da sauya sheka daga APC zuwa Labour Party domin goyon bayan Peter Obi
  • Ya ce tsohon gwamnan Anambra yana da gogewar da 'yan Najeriya ke buƙata domin tsamo su daga halin da ake ciki

Ondo - Gabanin babban zaɓen 2023 nan da yan kwanaki, ɗan takarar da ya nemi tikitin jam'iyyar APC na majalisar tarayya a jihar Ondo, Honorabul Stephen Adeyeri, ya sauya sheka zuwa Labour Party.

Jaridar Tribune tace yayin da yake jawabi kan matakin da ya ɗauka, Adeyeri ya ce ya yi haka ne bayan gano Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a LP, zai iya ceto Najeriya.

Sauya sheka a Ondo.
Babban Jigon Jam'iyyar APC A Jihar Ondo Ya Sauya Sheka Zuwa LP Hoto: tribuneonline
Asali: Facebook

A cewarsa, Obi, tsohon gwamnan Anambra ya nuna wa duniya manyan dalilai kan yadda za'a ja ragamar Najeriya ta matsa zuwa mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Ya ce Peter Obi ya cancanci samun duk goyon bayan da ya dace domin ya kai ga cika burrin zama shugaban kasa a zaɓen watan Fabrairu kana ya dawo da martabar Najeriya a duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mista Adeyeri ya bayyana cewa shi da ɗumbin magoya bayansa sun cimma matsayar barin APC ne da komawa inuwar LP domin yin aiki tukuri wurin tabbatar da nasarar Obi.

A cewarsa, "Najeriya na bukatar Injiniyan kuɗi kamar Obi domin warware kalubalen tattalin arziki da ya hana kasar samun ci gaba."

"Dan takarar LP yana da kwarewa da gogewar da zai iya sauya matsin da ake ciki kuma ya kawo waraka ga matsaloli kama daga karancin Fetur, rashin wuta, yunwa da sauran kalubalen da suka hana mutane sakat."

Da yake maraba da masu sauya shekar, Sakataren LP a Ondo, Mista Abiodun Agbaje, ya roke su da su haɗa hannu da sauran mambobi su tabbatar LP da 'yan takararta sun lashe zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ɗan Takarar Gwamna a 2023 Kazamin Hari, Sun Bude Masa Wuta

Ya kuma roki su rungumi kamfen gida-gida a dukkan ƙananan hukumomin jihar, inda ya ƙara da cewa LP ce jam'iyya mai nasara, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An kaiwa ɗan takarar gwamnan SDP hari

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai kazamin hari kan tawagar ɗan takarar gwamna a jihar Ribas

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bude wa tawagar kamfen ɗan takarar wuta a Akinima, kamar hukumar Ahoada ta yamma ranar Litinin.

A wnai gajeren bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, an hangi tawagar kamfen na turereniyar neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262