Buhari: Babu Gwamnati Tilo da Zata Iya Magance Matsalolin Najeriya

Buhari: Babu Gwamnati Tilo da Zata Iya Magance Matsalolin Najeriya

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa babu gwamnati daya tilo da ta isa ta shawo kan matsalolin Najeriya
  • Ya sanar da hakan ne a taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya wanda aka yi a jiya a Abuja inda yace Najeriya tana tsaka mai wuya
  • Ya sanar da cewa, ana bukatar kokarin da gwamnatocin baya suka yi inda za a gina a kansu don samun Najeriya da kowa ke fatan samu

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin yace babu gwamnati daya da za ta iya magance dukkan matsalolin Najeriya.

Shugaba Buhari
Buhari: Babu Gwamnati Tilo da Zata Iya Magance Matsalolin Najeriya. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari a yayin zantawa kan halin da tsaro, tattalin arziki da shari'a ke ciki a Abuja, ya bayyana cewa, kokarin da gwamnatocin baya suka yi ake bukata domin shawo kan matsalolin kasar nan, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Duk da Barazanar Tsaro, Shugaba Buhari Ya Dura Kano, Zai Kaddamar da Jerin Ayyuka

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kasan yayi fatan cewa taron, wanda Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta shirya, zai bada gudumawa wurin cigaban Najeriya.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya tunatar da lauyoyin kan cewa kasar nan tana da hakki a kansu.

A kalamansa:

"Wannan ce hanyar da za a bi. Ina so in gode muku kan yadda ku ka dawo da burin 'yan Najeriya. Ina son yarda cewa kungiyar za ta samar da shugabancin da ya dace. Ina fatan a yayin tattaunawarmu, za mu fitar da tsarin da zai samar da mahanga ga mulki mai zuwa.
"Zan iya cewa babu gwamnati a kasar nan da za ta iya shawo kan matsalolin Najeriya. Amma a yayin da muke gini kan ginshikin da tsofaffin gwamnatoci suka yi, ba za mu yi watsi da dukkan abinda suka gina ba, sai mu dora mu gina Najeriya da muke so.

Kara karanta wannan

Akwai Babban Tanadi Da Na Yi Wa Yan Arewa Idan Na Zama Shugaban Kasa, Obi

“A matsayin gwamnati, abinda aka tattauna za a iya aiko mana da shi, wannan zai iya zama wani bangare na takardun da zamu shirya yayin mika mulki ga gwamnati mai zuwa."

Ganduje ya ziyarci Buhari a Daura, yace Kanawa sun shirya tarbarsa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci Shugaba Buhari a garin Daura ranar Lahadi da ta gabata.

Ya yabawa shugaban kasan kan azancin da yayi na dage wa'adin daina amfani da tsofaffin kudi a kasar nan har zuwa ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.

Yace jama'ar Kano sun shirya tsaf domin karbar bakuncin shugaban kasan a jihar yayin da zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng