2023: Tun Farko Ban Tare da Bola Tinubu a APC, Naja’atu ta Bayyana ‘Dan Takaranta
- Naja’atu Mohammed ta ce tun da aka kada gangar siyasa, ba ta goyi bayan Bola Tinubu a APC ba
- ‘Yar siyasar ta ce Farfesa Yemi Osinbajo ta goyi baya a zaben tsaida gwani na ‘dan takaran Jam’iyya
- Ganin Osinbajo bai kai labari ba, Hajiya Naja’atu Mohammed ta ce ta fita daga harkar siyasar
Abuja - Naja’atu Mohammed wanda ‘yar gwagwamarya da siyasa ce wanda tayi fice a Najeriya, tayi hira da Punch a game da matsayarta a kan zaben 2023.
Hajiya Naja’atu Mohammed ta shaidawa jaridar dalilinta na kin goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu da dalilinta na gujewa yakin neman zaben Tinubu/Shettima.
‘Yar siyasar ta ce tana cikin wadanda suka rika tunzura mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi tikitin jam’iyyar APC a zaben bana.
Dalilin fitacciyar ‘yar siyasar kuwa shi ne Osinbajo Farfesa ne mai ilmi, wanda ya san ya kamata, bugu da kari ta ce bai tsufa da rike shugabancin Najeriya ba.
Yemi Osinbajo na so a APC - Naja'
"Bari in fada abin da ya faru tun farko, ban goyi bayan Tinubu a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa ba, Farfesa Yemi Osinbajo na marawa baya tun tuni.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kai har mutane na tura domin su zuga Yemi Osinbajo ya nemi tikiti, ganin yana da sauran shekaru, yana da ilmi, yana daukar mataki, sannan yana da basira.
Mun lura a duk lokacin da Buhari ya bar Najeriya, sai abubuwa su soma yin kyau, har da darajar Naira"
- Naja’atu Muhammad
Magudi a zaben tsaida gwani
Da Bola Tinubu ya lashe zabe, ya ci nasara ne ta mafi munin hanya. Na san yadda aka damkawa masu zaben tsaida gwani kudi domin su kada kuri’a.
Baro-baro aka rubuta sunan Asiwaju, an biya su kudi ne su je su kada sunansa a cikin akwati. Saboda wannan na yi watsi da zaben fitar da gwanin (APC).
- Naja’atu Muhammad
Meya biyo bayan zaben gwani?
Naja’atu ta shaidawa jaridar yadda Hon. James Faleke ya gayyace ta domin taya Bola Tinubu kamfe, amma ta nuna ba ta da sha’awar goyon bayan takararsa.
Mutumiyar Kanon ta ce a karshe ta bukaci ta zauna da Tinubu kafin ta dauki matsaya, a cewarta sun zauna a Landan, ‘dan takaran ya yi ta gyangyadi.
Tasirin canjin kudi
Rahoto ya zo a safiyar Litinin, inda aka fahimci Asiwaju Bola Tinubu ya taka rawar gani wajen ganin an tsawaita wa’adin canza tsofaffin kudi a Najeriya.
‘Dan takaran na jam’iyyar APC a 2023 ya sanar da Duniya hakan da ya ziyarci Sarkin Benin, ya ce da bai tsoma baki CBN ya kara lokaci ba, da bai kyauta ba.
Asali: Legit.ng