Sai Da Goyon Baya Na Atiku Zai Samu Kuri'u A Jihar Oyo: Abokin Wike, Gwamna Makinde

Sai Da Goyon Baya Na Atiku Zai Samu Kuri'u A Jihar Oyo: Abokin Wike, Gwamna Makinde

  • Daya daga cikin gwamnonin G5 masu fito-na-fito da uwar jam'iyyar PDP ya yi magana kan Atiku
  • Oluseyi Makinde na neman zarcewa kan kujerarsa na gwamnan jihar Oyo a zaben 2023 mai zuwa
  • Gwamnonin biyar sun balle daga kamfen jam'iyyar PDP kuma sun ce ba dasu Atiku zai yi nasara ba

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya jinjinawa gwamnonin arewa na jam'iyyar All Progressive Congress APC bisa amincewa mulki ya koma kudancin Najeriya.

Makinde, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin hira da Seun Okinbaloye na ChannelsTV yayin shirin 'Politics Today'.

Ya ce gwamnonin APC na Arewa sun yi matukar burgesa lokacin da suka nuna goyon bayansu ga dan kudu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa:

"Wajibi ne na yabawa gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnoni irinsu Nasir El-Rufa'i, Gwamnan jihar Jigawa (Badaru Abubakar), Mai Mala Buni (na Yobe), Gwamnan Kogi (Yahaya Bello)."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023

"Sun hada kansu a cikin gida kuma suka ce don hadin kan kasar nan, mu hakura da manufofinmu. Mulki ya koma kudu. Saboda haka wajibi ne a jinjina musu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Amma mu a jam'iyyarmu me ya fari? Muna ta fada da juna kuma cewa ayi watsi da kundin tsarin mulkin mu. Ban tunanin haka ya dace."
Makinde
Sai Da Goyon Baya Na Atiku Zai Samu Kuri'u A Jihar Oyo: Abokin Wike, Gwamna Makinde Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamnan ya ce dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, na amfani da nasarorin da ya samu a jihar wajen kamfe.

A cewarsa, sai da goyon bayansa Atiku zai samu nasara a zaben.

Yace:

"Idan dan takararmu (Atiku) na son nasara a jihar Oyo, sai na yi masa kamfe saboda PDP a jihar na amfani da nasarorin da mukayi cikin shekaru uku da suka gabata."

Gwamna Makinde na cikin gwamnonin G5 dake adawa da Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

2023: "Dole Sai Da Ni" Gwamnan G-5 Ya Maida Martani Mai Dumi, Ya Fallasa Wani Shirin Atiku

Sauran sun hada da Nyesom Wike na River, Samuel Ortom na Benue, Ikezie Ikpeazuna Enugu da Ifeanyi Uguwanyi na Abia.

Muna nan zaku gani Atiku ba zai lashe zaben 2023 ba, Wike

Shugaban kungiyar gwamonin G5 Gwamna Nyesom Wike, ya ce tun kan Atiku Abubakar ya hau mulki ya fara yi masa barazanar da bita da kulli.

Ya ce saboda haka sun nan ba zasu bari Atiku yayi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel