Kanin Dan Takarar Gwamnan NNPP a Bauchi da Wasu Kusoshi Sun Koma PDP
- Wata ɗaya da wasu kwanaki kafin zaben gwamnoni, ɗan takarar NNPP a Bauchi ya rasa manyan yan siyasa da makusantansa
- Kanin mai neman zama gwamna a inuwar NNPP da wasu kusoshin siyasa sun koma PDP a taron Ganjuwa
- Gwamna Muhammed na PDP ya nuna farin ciki da lamarin, inda yace alama ce ta mutane na son mulkinsa
Bauchi - Buhari Jika, kanin ɗan takarar gwamnan New Nigeria People Party a jihar Bauchi, Halliru Jika da wasu 'yan uwansa sun sauya sheƙa zuwa PDP mai mulki.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sun koma jam'iyyar PDP mai mulkin Bauchi domin su marawa kudirin neman tazarcen gwamna Bala Muhammed.
Haka zalika, Ko-oditenan yakin neman zaben tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abubakar, watau Auwalu Ganjuwa, da shugaban ƙungiyar 'yan takara na jiha, Abbas Barde, sun koma PDP.
Jiga-jigan siyasar sun sanar da sauya shekarsu a wurin gangamin kamfen Kauran Bauchi wanda ya gudana ranar Jumu'a a Kafin Madaki, ƙaramar hukumar Ganjuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa suka yanke komawa PDP?
Masu sauya shekar sun ce sun ɗauki wannan matakin ne bisa ganin tubalin ci gaba da gwamna Mohammed ya dora a Bauchi wanda ya kama hanyar sauya jihar.
Baya ga haka sun kuma zargi Sanatan Bauchi ta tsakiya, Haliru Jika, da ƙin agaza wa gwamna Muhammed ta hanyar jawo ayyukan raya ƙasa daga gwamnatin tarayya zuwa shiyyarsu.
Bugu da ƙari, jiga-jigan siyasan sun bayyana cewa tuni suka kammala shirin tara magoya baya domin cika burin tazarcen gwamna mai ci wanda haka ne kaɗai zai ba shi damar ci gaba da ayyukan da ya faro.
Da yake maraba da mutanen, Gwamna Muhammed ya yi na'am da sauya shekar inda ya kira matakin da suka ɗauka a matsayin wata alamar yarda da salon mulkinsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun kafin fara Ralin, gwamnan ya yi yawon duba ayyukan Tituna da suka haɗa gariruwa da ƙauyuƙa a sassan ƙaramar hukumar.
A wani labarin kuma Gwamnonin G-5 Sun Bayyana 'Yan Takarar Da Zasu Marawa Baya a Zaben 2023
Har yanzun dai babu alamun cewa za'a haɗa inuwa ɗaya tsakanin Atiku ɗa gwamnonin tawagar G-5 a PDP gabanin watan Fabrairu.
Gwamnonin su halarci Ralin PDP a jihar Enugu kuma sun sha alwashin.taimaka masu su ci zaɓe amma sun yu gum game da batun Atiku.
Asali: Legit.ng