Atiku Na Shiga Rigunan Ayyukan Mu Domin Samun Nasara a Oyo, Makinde
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya maida martani ga kalaman tsohon ministan makamashi da karafa, Wole Oyelese
- Makinde, ɗaya daga cikin gwamnonin PDP da suka kafa tawagar G-5, ya ce Atiku na bukatarsa kafin ya ci Oyo
- Har yanzun ba'a samu masalaha ba a tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar PDP yayin da zabe ke kara matsowa
Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce nasarorin da gwamnatinsa ta samu Atiku Abubakar ke amfani da su domin samun nasara a jihar a zaɓe mai zuwa.
Gwamna Makinde ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake jawabi a cikin shirin Politics Today na kafar Channels TV ranar Jumu'a 27 ga watan Janairu, 2023.
Makinde, matashin gwamna daga cikin tawagar G-5, ya yi wannan furuci ne yayin martani ga kalaman tsohon ministan makamashi da ƙarafa, Wole Oyelese.
Da yake sukat gwamnan da abinda ya kira yaudara domin amfana da Atiku, Mista Oyesele, ya bayyana cewa Makinde na bukatar Atiku idan yana son ci gaba da mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma gwamnan Oyo ya maida martani ga tsohon ministan ɗan asalin jihar Oyo da cewa abun ba haka yake ba, ya faɗi zancen a juye.
A kalamansa, Makinde ya ce:
"Yaya Oyesele ya girme ni a shekaru kuma ba zan yi wani abu na rashin ladabi garesa ba. Amma a tunanina maganar an sa dabaru a ciki, ya faɗi maganar a juye."
"Idan ɗan takararmu na son cin zabe a Oyo, yana bukatar na yi masa kamfe domin PDP a jihar Oyo na taƙama ne da ayyukan da muka zuba wa mutane a shekaru uku da wasu burbushi."
"Dan haka yana kokarin a ba shi muƙamin Minista, kuma ina ganin ba wanda zai naɗa shi minista domin a ba ya da aka ɗora shi, bai tabuka komai ba."
Makinde ya kara da cewa bukatun tawagar G-5 a jam'iyyar PDP ya zarce burikan kai da kai, gwamnonin na fafutuka ne kan rashin adalcin shugabannin jam'iyya, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.
Tinubu Ya Ɗauki Alkawari Kan Yan Gudun Hijira, Ya Ƙalubalanci Atiku Kan Abu 1 Tak
A wani labarin kuma Bola Tinubu ya ɗauki alkawarin maida 'yan gudun Hijiɗa gidajensu idan ya zama shugaban ƙasa
Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya ce babu dalilin da zai sa mutane su ci gaba da zama matsugunan 'yan gudun Hijira a ƙasarsu ta gado.
Asali: Legit.ng