Kotu Ta Tsige Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, Ta Ba APC Nasara

Kotu Ta Tsige Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, Ta Ba APC Nasara

  • A yau babban kotu dake jihar Osun ta yanke hukuncin farko kan sahihin wanda lashe zaben jihar Osun
  • Alkalan Kotun sun ce Ademola Adeleke ba shi bane halastaccen wanda ya samu nasara a zaben ba
  • Adeleke yanzu yana da damar garzayawa kotun daukaka kara domin neman sharhi da gyara

Osogbo - Kotun zaben gwamnan jihar Osun dake zama a Osogbo ta sallami gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, matsayin gwamnan jihar.

Kotun ta baiwa Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC nasara, rahoton Vanguard.

Alkalan kotun biyu sun ce sun gamsu da hujjojin APC saboda haka a sallami gwamnan daga ofis, yayinda alkali 1 yace bai gamsu da hujjojin ba.

Kotun a karshe ta umurci hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta kwace takardar shaidan nasara daga hannun Adeleke kuma a baiwa tsohon gwamna Adegboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

2023: Abokin Takarar Atiku Ya Fasa Kwai, Ya Faɗi Manyan Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Samu Nasara a Shiyyoyi 2

Shugaban kwamitin alkalan, Justice Tertse Kume, ya ce Oyetola ne sahihin wanda ya samu nasara da kuri'u 314,931 yayinda Adeleke ya samu 219,666.

Oyetola
Kotu Ta Tsige Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, Ta Ba APC Nasara
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar INEC a watan Yuli da akayi zaben ta sanar da cewa Adeleke ya samu nasara da kuri'u 403,371. Ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30.

Shi kuwa Oyetola INEC tace ya samu kuri'u 375,027 inda lashe kananan hukumomi 13.

Kai tsaye ya shigar da kara kotu inda yayi zargin cewa an tafka magudi a rumfunan zabe 749.

Hakazalika ya bayyana cewa Adeleke takardun makaranta na bogi ya baiwa hukumar INEC.

An fara zaman kotun ne a watan Agusta, 2022, yan makonni bayan zaben gwamnan.

Oyetola, wanda ke kan mulki a lokacin ya dauki Lateef Fagbemi da Akin Olujimi matsayin lauyoyinsa.

Yayinda Adeleke da PDP suka sauki Alex Iziyon da Onyeachi Ikpeazu matsayin lauyoyinsu.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Kotu ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Karshe kan Zaben Gwamnan Osun

Mun kawo muku cewa kotun sauraron kararrakin zabe da ka zama a jihar Osun ta sanar da cewa za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar da aka yi na 2022

Kamar yadda takardar da kotun ta lika a gaban dakin kotun, tace za ta fara zaman kotun da karfe 9 na safiyar 27 ga watan Janairun 2022

Tsohon gwamnan jihar, Oyetola tare da jam'iyyar APC ta maka Adeleke a kotu kan zargin aringizon kuri'u a zaben jihar da ya gabata wanda yayi nasara

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel