'Dan Takarar Gwamna a Fitacciyar Jihar Arewa ya Ya Kwanta Dama
- Alhaji Aliyu Maina, 'dan takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar National Rescue Movement, NRM, ya kwanta dama
- Maina ya rasu ne bayan rashin lafiya da yayi fama da ita a babban birnin tarayya da ke Abuja inda jam'iyyar NRM ta tabbatar
- Sakataren jam'iyyar na kasa yayi kira ga 'yan uwa, abokan kasuwanci da na siyasa da suka kasance da iyalan mamacin a wannan lokacin alhini
Adamawa - 'Dan takarar gwamnan a jam'iyyar National Rescue Movement a jihar Adamawa, Alhaji Aliyu Maina, a ranar Alhamis an tabbatar da mutuwarsa, ana sauran wata daya zabe.
Ya rasu a ranar Laraba, 25 ga watan Janirun 2023 bayan fama da rashin lafiya da yayi a Abuja, rana daya da 'dan takarar gwamnan jihar Abia, Farfesa Uchenna Ikonne, na jam'iyyar PDP ya mutu.
Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar NRM, Olusola Afuye, ya tabbatar da hakan a takardar da ya aikewa jaridar Punch.
Yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kamar yadda takardar da iyalansa suka sanar, marigayi Alhaji Abba Maina ya rasu a ranar laraba, 25 ga watan Janairu a gidansa na babban birnin tarayya da ke Abuja bayan fama da rashin lafiya.
"Tuni aka yi jana'izar tare da birne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Muna fatan Allah ya kare iyalansa da dukkan masoyansa.
"Muna kira ga dukkan iyalansa, abokan kasuwanci da na siyasa da su nuna kauna ga iyalan Maina da kulawa a yayin wannan makokin."
"Za a samu karin bayani inda za a bayyanawa jama'a bayan tattaunawa da taruka da iyalansa da iyalansa na siyasa kan mataki na gaba."
Fusatattun matasa sun tada zanga-zanga bayan zuwan Buhari Katsina
A wani labari na daban, wasu fusatattun matasa a jihar Katsina sun balle zanga-zanga bayan Shugaba Buhari ya kaddamar da gadar sama ta Kofar Kaura da ke birnin Katsina.
Sun fara kona tayoyi a titin da aka kaddamar inda jami'an tsaro suka hanzarta dakile lamarin.
Matasan sun dinga ihun bamu yi, tare da jifan jami'an tsaro da kuma motocin APC da suke wucewa.
Tuni 'yan sanda suka baza musu barkonon tsohuwa inda suka tarwatse baki daya.
Asali: Legit.ng