Rai 1 ya Salwanta Yayin da 'yan Daba Suka Cukume da Fada a Ralin APC na Jigawa

Rai 1 ya Salwanta Yayin da 'yan Daba Suka Cukume da Fada a Ralin APC na Jigawa

  • Wani matashi ya rasa ransa sanadiyyar wani rikici da ya rincabe tsakanin kungiyoyin matasan jam'iyyar APC a Jigawa yayin zagayen kamfen a karamar hukumar Kazaure
  • An ruwaito yadda rikicin ya barke yayin zagayen wanda ya yi sanadiyyar asarar rai guda, inda tuni wanda ake zargin ya tsere jihar Kano
  • Sai dai, mazauna yankin sun yi zanga-zanga gami da zargin 'dan takarar sanatan Arewa maso yamma, Babangida Hussaini da tara 'yan daba don rushewar zaman lafiyan yankin

Jigawa - Wani mutumi ya rasa ransa a jihar Jigawa ranar Talata a zagayen kamfen don APC cikin karamar hukumar Kazaure.

Taswirar Jigawa
Rai 1 ya Salwanta Yayin da 'yan Daba Suka Cukume da Fada a Ralin APC na Jigawa. Hoto daga premiumtimes.ng
Asali: UGC

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Ekot, ya shaida wa Premium Times yadda 'yan sanda ke dakon wanda ake zargi da kisan da ya tsere zuwa jihar Kano da ke makwabtaka dasu bayan aikata laifin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

"'Yan sanda suna kan binciken lamarin, babban wanda ake zargin ya tsere Kano. Rikici ne cikin jam'iyya da magoya bayan wani 'dan takara suka samu sabani. Duk 'yan jam'iyyar APC ne ba rikici bane tsakanin jam'iyya da jam'iyya."

- A cewar kwamishinan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ne ya jagoranci zagayen kamfen din a Kazaure ranar inda rikici ya barke tsakanin kungiyar matasa magoya bayan APC da ke da jikakka tsakaninsu har yayi sanadiyyar mutuwar wani.

Premium Times ta tattaro yadda marigayin ya ke gayon bayan 'dan takarar sanata na jam'iyyar a yankin Arewa maso yamma, Babangida Hussaini.

Mazauna yankin sun bayyana sunan mamacin da Halliru Lafka, mazaunin anguwar Kazaure.

Kisan ya janyo zanga-zanga daga mazauna yankin da suka kona fostocin 'dan takarar, Hussaini, wanda suka zargesa da hayar 'yan bangan siyasa da 'yan sara suka don tarwatsa kwanciyar hankali da zaman lafiyar anguwar.

Kara karanta wannan

Magoya Bayan PDP Sun Wanke Filin da Tinubu Yayi Kamfen a Jigawa, Sun ce Najasa Suka Wanke Tas

Sai dai, lambar Hussaini ba ta shiga don jin ta bakinsa game da lamarin har zuwa yammacin Laraba.

Jigawa: Magoya bayan PDP sun wanke filin da APC tayi rali

A wani labari na daban, magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa sun yi gangami tare da wanke filin da Bola Ahmed Tinubu yayi ralinsa a jihar.

Sun bayyana cewa, sun wanke fatara, rashin tsaro da sauran matsalolin kasar nan da APC ta kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel