Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

  • Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta Jihar Imo ta dakatar da kamfe da sauran tarurukan siyasa
  • Sanarwar da sakataren watsa labarai na APC a Imo, Cajetan Duke, ya fitar ta ce an yi hakan ne saboda saboda mutuwar shugaban karamar hukuma na Ideato na Arewa
  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka halaka Honarabul Chris Ohizu, ana zargin kisansa na da alaka da siyasa

Jihar Imo - Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a Jihar Imo ta dakatar da yakin neman zabenta, da taron jin ra'ayin mutane da wasu harkoki a kananan hukumomin jihar Imo, rahoton Nigerian Tribune.

A sanarwar da jam'iyyar ta fitar a ranar Laraba a Owerri ta bakin sakataren watsa labarai, Cajetan Duke, ya ce an dakatar da kamfen din ne biyo bayan kisar gilla da aka yi wa Hon. Chris Ohizu, shugaban karamar hukumar Ideato ta Arewa.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Da Tunani Irin Na Sarakunan Kama Karya, Naja'atu Ta Tono Bakin Shafin Dan Takarar APC

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC Ta Dagatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar ta ce umurnin dakatarwa ta zo ne daga gwamnan a matsayinsa na ciyaman din kwamitin kamfen din jam'iyyar APC a jihar, don girmama shi.

Ya ce:

"Yayin da muke alhinin rashin Hon Ohizu, da sauran yan jam'iyya maza da mata da sauran mutanen Imo da suka rasa ransu bisa rashin tsaro mai alaka da siyasa a jihar mu, muna mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa."

Ya bada tabbacin cewa jam'iyyar za ta cigaba da bada tallafi kan kokarin gwamnatin jihar da sauran hukumomin tsaro na ganin an gano wadanda suka yi wannan mummunan abin an hukunta su.

Mai magana da yawun jam'iyyar ya ce nan gaba za a fitar da sabon jadawalin harkokin jam'iyyar, ya nemi afuwa bisa sauyin.

Yar Takarar Kujerar Mataimakin Gwamna Ta Fita Daga APC Ta Koma PDP

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana tsadar abinci, dakin ajiyan kamfanin abinci ya kone kurmus

Kun ji cewa, Helen Boco, tsohuwar yar takarar kujerar mataimakiyar gwamnan a zaben shekarar 2019 a jihar Cross Rivers a APC ta koma jam'iyyar PDP.

A cewar wani rahoto da Trinune Online ta wallafa, Boco ta sauya shekar ne yayin da ya rage kwana 49 a yi babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Ta yi korafin cewa duk da muhimmin gudunmawa da ta bada wurin gina jam'iyyar APC, shugabannin jam'iyyar sun mayar da ita saniyar ware.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164